Okwagbe gari ne na kasuwanci a karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, Najeriya.[1] Garin yana kusa da Kogin Forçados, kuma yana da iyaka da garuruwan Oginibo, Okuemor, Otegbo, Owahwa, Egbo-Ide, da Okreka (Ofonibaya), da dai sauransu. Okwagbe shine birni mafi yawan jama'a a Ughelli ta Kudu, kuma ana ɗaukarsa a matsayin cibiyar kasuwanci. Yanayin kasuwa ne ya janyo sunan garin, wanda ke nufin "taruwa."

Okwagbe

Wuri
Yawan mutane
Harshen gwamnati Turanci
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Akwai makarantun firamare na gwamnati guda biyu. okwagbe, makarantar sakandare na gwamnati ɗaya, sakandaren mishan guda ɗaya, cibiyar kiwon lafiya ta gwamnati, dakunan shan magani masu zaman kansu, manyan kasuwa biyu, ofishin ‘yan sanda ɗaya, wurin binciken sojoji, da kuma gidajen ten quarters, wanda kuma aka sani da tituna.

An raba garin zuwa unguwanni biyu: Okwagbe doron kasa da kuma Yankin ruwa na Okwagbe.

Manazarta gyara sashe

  1. "List of Towns and Villages in Ughelli South LGA". Nigeriazipcodes.com.