Adebayo Salami wanda aka fi sani da Oga Bello (an haife shi 9 ga watan Mayun 1952), gogaggen ɗan wasan kwaikwayo ne, mai shirya fina-finai, kuma darakta.[1][2][3]

Oga Bello
Rayuwa
Haihuwa jahar Lagos, 9 Mayu 1953 (71 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yaren Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a jarumi, darakta, editan fim, mai tsara fim, marubin wasannin kwaykwayo da marubucin wasannin kwaykwayo
Muhimman ayyuka Omo Ghetto: The Saga
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm2104761
oga bello

Adebayo yana da aure da mata biyu da ƴaƴa goma sha takwas (ƴaƴa maza 9 da mata 9)[4]

Ko da yake Salami ɗan asalin jihar Kwara ne, an haife shi a ranar 9 ga watan Mayun 1953 a jihar Legas inda ya yi karatunsa na firamare da sakandare.[5]

Ya fara aikin wasan kwaikwayo a shekarar 1964, tare da wata ƙungiya mai suna Young Concert Party, ƙarƙashin jagorancin Ojo Ladipo, wanda aka fi sani da Baba Mero. Bayan ƴan shekaru, ƙungiyar ta canza suna zuwa rukunin gidan wasan kwaikwayo Ojo Ladipo, daga baya kuma ta koma Awada Kerikeri Theatre Group.[6] Bayan rasuwar Ojo Ladipo a shekarar 1978, Salami ya ɗauki rigar shugabancin ƙungiyar, wanda ya kai shi ga shahara.[7]

Ya fito a fim ɗin Yarbanci na farko, Ajani Ogun, inda marigayi Adeyemi Afolayan, mahaifin Kunle Afolayan da Gabriel Afolayan, ke taka rawa.[8]

Ya kuma fito a wani fim mai suna Kadara na Adeyemi Afolayan (Ade love).[9] Daga baya ya fito a cikin fitaccen shirin barkwancin Najeriya na barkwanci rabin awa mai suna Oga Bello.[10]

Ya shirya fim ɗinsa na farko, Ogun Ajaye, a shekarar 1985, daga bargon Awada Kerikeri.[11]

Tun shekarar 1985, ya shirya, bayar da umarni da kuma fitowa a cikin fina-finan Yarbawa da dama.[12]

 
Oga Bello

Ya kasance memba na farko na Association of Nigerian Theater Arts Practitioners,[13] kuma ya zama shugaban ƙungiyar.

  • 2014 Mafi kyawun Kyautar Nollywood[14]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.premiumtimesng.com/entertainment/nollywood/171120-theatre-arts-movie-practitioners-celebrate-veteran-actor-adebayo-salami.html
  2. https://m.thenigerianvoice.com/movie/30122/3/i-was-beaten-blue-black-for-acting-oga-bello.html
  3. https://thenationonlineng.net/popular-film-star-oga-bello-loses-mum/amp/
  4. https://www.legit.ng/1414306-adebayo-salami-oga-bello-biography-age-family-net-worth.html
  5. https://web.archive.org/web/20150101040056/http://www.voiceofnigeria.org/nigeria/actor-advocates-promotion-of-indigenous-languages.html
  6. https://web.archive.org/web/20150101035551/http://sunnewsonline.com/new/?p=76970
  7. https://web.archive.org/web/20150101072654/http://leadership.ng/entertainment/384685/parents-almost-cursed-taking-acting-oga-bello
  8. https://web.archive.org/web/20150101035500/http://www.mynewswatchtimesng.com/oga-bello-tells-career-family-kids/
  9. https://web.archive.org/web/20150101044456/http://e247mag.com/adebayo-salami-oga-bello-returns-to-stage-with-olokooba-at-50/
  10. https://archive.ph/20141231232355/http://www.ngrguardiannews.com/saturday-magazine/celebrity/190904-more-pips-for-the-legendary-oga-bello
  11. https://web.archive.org/web/20150101024102/http://www.punchng.com/feature/life-times/my-friends-taught-me-because-i-couldnt-go-to-school-oga-bello/
  12. http://thenationonlineng.net/new/oga-bello-why-younger-nollywood-stars-go-broke-easily/
  13. https://web.archive.org/web/20150101040115/http://dailyindependentnig.com/2014/02/tamapan-house-of-division-and-cheap-nollywood-politics/
  14. http://thenationonlineng.net/new/bon-awards-to-honour-liz-benson-adebayo-salami-others/