Ndow Niang (an haife ta a ranar 20 ga watan Agusta 1954) ɗan wasan tseren (middle-distance) Senegal. Ta yi takara/gasa a tseren mita 800 na mata a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 1976 . [1] Ita ce mace ta farko da ta wakilci ƙasar Senegal a gasar Olympics.[2]

Ndew Niang
Rayuwa
Haihuwa 20 ga Augusta, 1954 (69 shekaru)
ƙasa Senegal
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 
Nauyi 55 kg
Tsayi 174 cm

Niang ta kasance 'yar wasan kwallon kafa, kuma ta kasance kyaftin din kungiyar Gazelles ta Dakar, babbar kungiyar mata a Senegal. A cikin watan Satumba na 1977, ƙungiyar ƙwararrun Faransa ta Red Star de Champigny Cœully ta sanya hannu; Kwanakin baya, ta lashe lambar zinare ta mita 1500 a gasar wasannin Afrika ta Yamma a Legas.[3]

Manazarta gyara sashe

  1. Evans, Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill; et al. "Ndew Niang Olympic Results". Olympics at Sports-Reference.com. Sports Reference LLC. Archived from the original on 2016-12-04.
  2. "First female competitors at the Olympics by country" . Olympedia . Retrieved 26 June 2020.
  3. Le Soleil (Dakar) 13th September 1977