Asibitin ƙashi na ƙasa na Igbobi
Asibitin ƙashi na ƙasa na Igbobi, asibiti ne a Legas, Najeriya. [1] Har ila yau, ana kiransa da sunan “igbobi” ko “asibitin igbobi”.
Asibitin ƙashi na ƙasa na Igbobi | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | jahar Legas |
Birni | Lagos, |
Coordinates | 6°31′52″N 3°22′13″E / 6.53123016°N 3.37018389°E |
History and use | |
Opening | 1945 |
Offical website | |
|
A cikin shekarar 2019, asibitin ya haɗu da SIGN Fracture Care International, Amurka don magance naƙasar hannu. [2]
Tarihi
gyara sasheAsibitin Orthopedic na ƙasa, na Igbobi, Legas ya fara aiki a matsayin cibiyar farfaɗo da sojojin da suka samu raunuka a yakin duniya na biyu a shekarar 1943, daga nan kuma ta ci gaba da zama asibiti ƙarƙashin kulawar likitocin Turawan mulkin mallaka na Burtaniya na Turawan mulkin mallaka na Najeriya a ranar 6 ga watan Disamba 1945. Asibitin wanda aka fara kiransa da Royal Orthopedic Hospital a shekarar 1956 ya kuma taka rawar gani wajen jinyar da sojoji da fararen hula da suka jikkata a yakin basasar Najeriya na shekarun 1967-1970. An mika asibitin ga gwamnatin jihar Legas a shekarar 1975 sannan kuma gwamnatin tarayya a shekarar 1979.[3][4][5]
Kiwon lafiya
gyara sasheAsibitin tana da ƙarfin ma'aikata kusan 1300. Tana da rukunin kulawa mai zurfi da iya aiki mai gadaje 450. Yanzu ana kyautata zaton asibitin a matsayin babban asibitin kashi a yammacin Afirka. Bankin Mobolaji Anthony ya ɗauki nauyin wani sabon sashe na asibitin wanda ya haɗa da gyaran sashen gaggawa.[3][5][6]
Asibitin yana da waɗannan sassan da aka jera don biyan buƙatun marasa lafiya [7]
Karamin Ministan Lafiya na lokacin, Dr Olorunnibe Mamora ne ya kaddamar da ɗakin jin daɗi da ke NOHIL wanda shi ne ɓangare mai zaman kansa na asibitin a ranar 1 ga watan Afrilu, 2021. An gina shi da kayan aiki na musamman don kulawa mai ƙima. Haka kuma a wannan rana, Modular Theatre mai suites shida an kuma kaddamar da aikin. [8]
A cikin shekarar 2022, an buɗe ɗakin gwaje-gwaje na kwayoyin halitta na zamani a asibiti don magance cututtuka kamar COVID'19 da yin gwaje-gwaje kamar PCR. [9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Edema, Grace (2022-08-16). "NOHIL unveils molecular laboratory". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-01-21.
- ↑ "National Orthopaedic Hospital Igbobi, partners experts on limb deformity". Vanguard. Retrieved 14 November 2023.
- ↑ 3.0 3.1 "National Orthopaedic Hospital Opens Skills Laboratory in Lagos". Channels Television. Retrieved 21 January 2016.
- ↑ Popoola Babalola (15 December 2015). "NBTE accredits Orthopaedic Hospital's college …as 96 nurses, health assistants graduate". The Vanguard.
- ↑ 5.0 5.1 Joseph Okoghenun (24 December 2015). "Igbobi hospital seeks improvement in health insurance, services". Nigerian Guardian. Retrieved 21 January 2016.
- ↑ "My challenges at Igbobi Orthopaedic hospital, by new MD". The Nation. 2 December 2008. Retrieved 21 January 2016.
- ↑ "News-NOHIL Management Board Commissions New Molecular Laboratory". www.nohlagos.gov.ng. Retrieved 2022-12-28.
- ↑ Obinna, Chioma (April 6, 2021). "Healthcare: FG building healthy system accessible to all, says Mamora". Vanguard. Retrieved November 14, 2023.
- ↑ Edema, Grace (2022-08-16). "NOHIL unveils molecular laboratory". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-01-21.