Ana samun mutanen Ndola a Taraba, Najeriya kuma suna cikin Kurmi da Ngada . Kaɗan kuma aka samu a Kamaru .

Mutanen Ndola

Bayan Fage gyara sashe

Ndola wata ƙabila ce ko ƙabilar mutanen da aka samo a jihar Taraba, Najeriya tare da kimanin mutane kusan dubu ɗari (100,000). Hakanan ana samun Ndola a Dodéo, Yankin Adamaoua a Kamaru kuma an ƙiyasta yawansu kusan 4,000. Ndola wani lokacin wasu mutane suna kiran shi Ndoro; Ndoola; Nundoro; yayin da Kamaru kuma ana kiranta Njoyame. Ndola yana cikin dangin yare na Benuwe-Congo, tare da rukunin iyaye na ƙabilun Mambiloid. Sauran ƙabilun da ke wannan rukuni wadanda suke da irin wannan fasahar magana sune: Mambila, Suga, Kwanja, Vute, Kamkam, Twendi da Wawa. Mafi yawan waɗannan yarukan ana samun su ne a yankin Mambila Plateau. Hakanan ana samun mutanen Ndola a cikin ƙananan yankunan Kurmi wanda shine mafi yawan yankunansu, Gashaka, Bali da Donga . A cikin Ƙaramar Hukumar Kurmi, mutanen Ndola suna da hedkwatarta, wanda ke Ba'Issa. Ba'Issa yana cikin kalmomi biyu: "Ba", kalmar Ndola, ma'anar Daddy, yayin da "Issa" sunan Hausa ne mai ma'anar Yesu. Sunan wanda ya fara zama kuma ya mallaki ƙasar ana kiransa Issa. Duk da kuma lokacin da maziyarta suka so ziyartarsa daga wasu ƙauyuka ko al'ummomin da ke kewaye da shi, koyaushe za su ce "Za mu je ganin Ba'Issa". Wannan Misalin ya samu karɓuwa daga mishan wanda ya fara zuwa yankin a farkon shekarar 1900.[1] Wannan shine sunan garin da ake amfani dashi har zuwa yau, kuma daga ƙarshe ya zama hedkwatar ƙaramar hukumar Kurmi.

Manazarta gyara sashe

  1. Rev. Elder Amos Adi (2005). "Brief History of the CRCN Baissa". crcn-ng.com. Archived from the original on 2016-02-22. Retrieved 2017-05-09.