Mutanen Akurmi (kuma Kurama ), ƙabilu ne Wanda suka fi yawa a cikin garin saminaka dake a jihar

Mutanen Akurmi
Mutanen Akurmi

Kaduna,da kuma jihar Kano da ke magana da harshen T'kurmi, yaren Kainji na Gabas ta Nijeriya .[1][2]wanda ke yankin arewa ta tsakiya.

Tarihi gyara sashe

Mutanen Akurmi, mutane ne masu sada zumunci waɗanda ke gudanar da sana'ar neman abinci, mazauna ne a jihar Kano, Filato da Kaduna kimanin shekaru 600 da suka gabata.

Addini gyara sashe

Akurmi akasarinsu mabiya addinin kiristanci ne, waɗanda yawansu ya kai 88.0% (tare da masu zaman kansu da kashi 30.0%, Furotesta 50.0% da Roman Katolika 20.0%). Ragowar masu bin addinin Kabilanci, 6.0% da Musulunci, 6.0%.

Sarauta gyara sashe

Ana samun Akurmi ne a cikin Akurmi (Kurama) Chiefdom a ƙaramar hukumar Lere . Ana kiran babban mai mulkin su " B'gwam Kurmi " ko Bagwama Akurmi. Sarkin da ke yanzu, HRH Dr. Ishaku S. Damina, B'gwam Kurmi II an ruwaito cewa gwamnan jihar Kaduna ya tsare shi a shekarar 2017. Hakanan ana kuma samun su a Saminaka Chiefdom a yanki ɗaya.

Manazarta gyara sashe

  1. Garba, Tom (March 26, 2017). "Akurmi Youth Ask El-Rufai To Release Kurama Chief". The Dream Daily. Retrieved September 12, 2020.
  2. "Why El-Rufai must not restructure Chiefdoms, Emirates - Association". August 2, 2017. Retrieved September 12, 2020.