Mai shari’a Musa Danladi Abubakar LLB, BL (an haife shi ranar 21 ga watan Nuwamba, 1958) lauyan Najeriya ne kuma babban alkalin jihar Katsina a yanzu daga 2018.[1] Shi ya rantsar da gwamnan jihar Katsina mai ci Rt. Hon. Alh. Aminu Bello Masari. Ya kasance shugaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Taraba wanda ya bayyana Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna mai cike da cece-kuce na shekarar 2015 a jihar Taraba.[2]

Musa Danladi Abubakar
Rayuwa
Haihuwa 1958 (65/66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a mai shari'a da Lauya

Kuruciya gyara sashe

An haifi Musa Danladi Abubakar a ranar 21 ga Nuwamba 1958 ga dangin 'yan kasuwanci a Funtua, jihar Katsina .[ana buƙatar hujja]

Ilimi gyara sashe

Abubakar ya fara karatunsa na farko a gidan mahaifinsa, inda ya koyi wasu ka'idoji na fikihu. Ya halarci makarantar firamare ta Aya, GSS Zaria, sannan ya yi GSS Funtua kafin ya koma Jami'ar Bayero University College wadda ta koma Jami'ar Bayero Kano daga 1978 zuwa 1981. Anan ne ya sami digirinsa a fannin shari’a kuma aka kira shi kungiyar lauyoyi na kasa a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya a wannan shekarar.[3]

Fara aiki gyara sashe

An nada Musa Danladi Abubakar a matsayin mai horar da shari’a kuma lauyan jiha da ke da hannu wajen gabatar da kara da bayar da shawarwarin shari’a a jihar Kaduna a lokacin tsakanin 1981 zuwa 1983. Ya shiga hidimar Kwalejin Nazarin Shari’a ta Jihar Kaduna, Katsina Campus a matsayin lacca a shekarar 1983. A shekarar 1983 – 1987 ya canza sheka zuwa aikin shari’a na jihar Kaduna, inda aka tura shi karamar hukumar Funtua a matsayin Alkali, daga nan kuma ya zama babban alkalin kotun majistare da aikin shari’a kan al’amuran da suka shafi farar hula da na laifuka da suka shafi kowane mataki. Katsina ta zama jaha a shekarar 1987 aka nada Musa Danladi a matsayin babban magatakarda tsakanin 1988 zuwa 1994 wanda yake rike da mukamin shugaban gudanarwa da kuma akawun bangaren shari’a; Magatakardar Probate kuma Sheriff na Jihar Katsina.[4]

Ya zama alkalin babbar kotu a shekarar 1994, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin babban alkalin jihar Katsina a shekara ta 2018. Abubakar shine babban alkalin jihar, kuma ya rantsar da Alhaji Aminu Bello Masari na yanzu.

Abubakar wanda ya lashe lambar yabo ta kasa a shekarar 1998, kuma memba ne a kungiyar lauyoyi na duniya, kuma dan cibiyar magance rikice-rikice ta kasa da kasa, Abubakar ya kuma taka rawar gani wajen ayyukan ci gaban al'umma daban-daban.[5]

Nadi a matsayin Babban Alkali gyara sashe

A ranar 13 ga watan Maris 2018 ne gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamnatin Aminu Bello Masari ta sanar da nadin Musa Danladi Abubakar a matsayin mukaddashin alkalin alkalai na jihar.[6][7] Daga bisani aka rantsar da shi a rana guda. Daga baya majalisar dokokin jihar Katsina ta tabbatar da shi a matsayin babban alkali a ranar 23 ga Mayu 2018.[8]

Rayuwa gyara sashe

Musa ya auri mata uku ya haifi ‘ya’ya goma sha bakwai; maza 11 da mata 6.[9]

Ayyukan al'umma gyara sashe

  • Majiɓinci kuma Amintacce ga ƙungiyoyin sa-kai da dama.
  • Daraktan Makarantar Kimiyya ta Ulul Al-bab da ke Katsina

Kyauta gyara sashe

An karrama shi matsayin Hon. LL. D (Hukuncin Shari'a) na Jami'ar Al-Nahda International University, Yamai a watan Nuwamba, 2018

Duba kuma gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "The Coming of Justice Musa Danladi Abubakar". ThisDay.
  2. "Tribunal sacks Taraba governor, Ishaku". Daily Trust. Retrieved 31 July 2021.
  3. Admin (21 July 2016). "ABUBAKAR, Musa Danladi". Biographical Legacy and Research Foundation. Retrieved 31 July 2021.
  4. Jibia, Abdussamad Umar (22 June 2020). "Katsina bandits: Why the chief judge should come clean". Blueprint Newspapers Limited. Retrieved 31 July 2021.
  5. Editor 3. "Justice Musa Danladi Abubakar Archives". National Accord Newspaper. Retrieved 31 July 2021.
  6. "Katsina gets new Chief Judge". Vanguard News. 13 March 2018. Retrieved 31 July 2021.
  7. Sijuade, Gbenga (13 March 2018). "Justice Musa Danladi Becomes Katsina State Chief Judge". Nigeria News. Retrieved 31 July 2021.
  8. "EXTRA: 4 interesting facts to know about Justice Musa Danladi, Katsina State's New Chief Judge". Katsina Post. 25 May 2018. Retrieved 31 July 2021.
  9. Ifeoma, Peters (3 September 2020). "Katsina Chief Judge Swears In 20 Sharia Court Judges - DNL Legal and Style". Retrieved 31 July 2021.