Munachim Alozie
Munachim Alozie | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Abiya, 1961 (63/64 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Munachim Ikechi Alozie ɗan siyasan Najeriya ne kuma ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga mazabar Obingwa/Osisioma/Ugwunagbo na jihar Abia a majalisar wakilai ta ƙasa ta 10. An haife shi a ranar 14 ga watan Afrilu, 1961 a Umuchima Akanu Ngwa da ke ƙaramar hukumar Ugwunagbo a jihar Abia.[1] Ya fara harkar siyasa ne a matsayin shugaban zartarwa na farko na ƙaramar hukumar Ugwunagbo daga shekarun 1997 zuwa 1998. Ya kuma kasance shugaban kwamitin riƙon kwarya na ƙaramar hukumar Ugwunagbo daga shekarun 2011 zuwa 2012 sannan kuma ya zama mataimakin shugaban kungiyar ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON) na ƙasa daga shekarun 1997 zuwa 1998.[1][2] Ya kasance, a lokuta daban-daban, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Abia ta Kudu, sannan ya zama Sakataren Kuɗi na PDP na Jiha. Hon Munachim Ikechi Alozie ya halarci Makarantar Firamare ta Akanu Ngwa, Makarantar Fasaha ta Sakandare, Obegu, da Kwalejin Aikin Noma (yanzu Imo State Polytechnic) Umuagwo. A Majalisar Wakilai ta Najeriya, Hon Munachim Ikechi Alozie yana riƙe da muƙamin shugaban kwamitin kwato kuɗaɗen gwamnati da aka kwace, aka ɓatar da su da kuma watsi da su a cibiyoyin hada-hadar kuɗi da hukumomin gwamnati, da kuma mamba a wasu kwamitocin majalisar.[1][3]
Aikin siyasa
gyara sasheAlozie ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Abia mai wakiltan mazaɓar Ugwunagbo na wa’adi biyu daga shekarun 2015 zuwa 2023. Shi ne Shugaban Masu rinjaye na gidan. Ya yi murabus daga wannan muƙamin ne a shekarar 2022 bayan ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar Labour Party, LP. [4] Ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Obingwa/Osisioma/Ugwunagbo a kan tikitin jam'iyyar LP a zaɓen majalisar wakilai na watan Fabrairu 2023 kuma ya yi nasara. [1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 "Otti congratulates Nwokocha, Onwusibe, urges Abians to be vigilant". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2023-03-02. Retrieved 2023-04-28. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ "No access roads in my constituency, says Chief Whip". 14 March 2022. Retrieved 28 April 2023.
- ↑ "No access roads in my constituency, says Chief Whip". 14 March 2022. Retrieved 28 April 2023.
- ↑ Emeruwa, Chijindu (2022-06-22). "2023: Abia Assembly appoints new Chief Whip as Munachim Alozie dumps PDP". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-04-28.