Mosobila Kpamma
Mosobila Kpamma ɗan siyasan Ghana ne kuma memba a majalisar dokoki ta farko a jamhuriya ta biyu ta Ghana mai wakiltar mazaɓar Talensi-Nabdam a yankin Upper Ghana a ƙarƙashin memba na Progess Party (PP).[1]
Mosobila Kpamma | |||
---|---|---|---|
1 Oktoba 1969 - 13 ga Janairu, 1972 District: Talensi Constituency (en) Election: 1969 Ghanaian parliamentary election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 1934 (89/90 shekaru) | ||
ƙasa | Ghana | ||
Karatu | |||
Makaranta | Tamale College of Education certificate (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Malami da ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Progress Party (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Mosobila a shekarar 1934. Ya halarci kwalejin horar da malamai ta Tamale. inda ya sami Takardar Horon Malamai daga baya kuma ya yi aiki a matsayin malami kafin ya shiga Majalisa.
Ayyuka da Siyasa
gyara sasheKpamma yayi aiki a matsayin malami kafin shiga siyasa. Ya fara harkokin siyasa ne a shekarar 1969 lokacin da ya zama dan takarar majalisar dokoki don wakiltar mazaɓar sa Talensi-Nabdam a yankin Upper Ghana kafin a fara zaɓen majalisar dokokin ƙasar ta Ghana a shekarata 1969 .
An rantsar da shi a majalisar farko ta Jamhuriya ta Biyu ta Ghana a ranar 1 ga Oktoban shekarar 1969, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen Ghana na shekarar 1969 da aka gudanar a ranar 26 ga Agusta 1969. kuma wa’adin mulkinsa ya ƙare a ranar 13 ga Janairun shekarata 1972.
Rayuwar mutum
gyara sasheYa kasance shugaba a garinsu, Kirista cikin imani.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ghana Year Book (in Turanci). Daily Graphic. 1971.