Moses Armah
Moses Armah 'Parker' Dan kasuwa ne dan kasar Ghana, mai kula da kwallon kafa kuma a halin yanzu shi ne mai kula da shugabancin Medeama SC da kuma shugaban rukunin kamfanonin Mospacka wanda ya hada da Medeama FM.[1]
Moses Armah | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa |
A watan Yulin na shekara ta 2010, dan kasuwar ya kammala karbe ikon Kessben FC akan kudi dalar Amurka 600,000 kuma ya sake mata suna Medeama SC. [2]
A yayin babban zaben kungiyar kwallon kafa ta Ghana na shekara ta 2019 Moses Armah ya wakilci Medeama SC a matsayin wakili kuma ya kada kuri'a a madadin kungiyar.[3]
Kafofin yada labarai na Ghana da dama sun ruwaito cewa yana da hannu a rikicin da tsohon dan wasan tsakiya na AC Milan Sulley Ali Muntari a lokacin gasar cin kofin duniya na FIFA a shekara ta 2014 da Ghana ta buga a Brazil.[4] A halin da ake ciki, a wata hira da gidan rediyon Ghana Happy FM Moses Armah a shekarar 2016 ya ce ya yafewa Muntari kan lamarin.[5] An kora Muntari zuwa gida da wuri daga sansanin Ghana tare da Kevin-Prince Boateng saboda lamarin. [6] Tsohon kocin Ghana James Kwesi Appiah ya bayyana cikakken bayani game da lamarin a littafinsa mai suna Leaders Don't have to Yell. [7]
Bayan samun Medeama a shekara ta 2010 Moses Armah ya ci gaba da daukaka martabar kulob din yayin da ya wakilci Ghana sau biyu a gasar kungiyoyin kwallon kafa ta Afirka ta hanyar taka leda a gasar cin kofin CAF Confederation a shekarun 2014 da 2016.[8][9]
Ya kuafa Wassaman FC wanda a watan Yuli 2013 aka canza mata suna zuwa Emmanuel Stars FC kuma Fasto TB Joshua ya siye ta.
Girmamawa
gyara sasheA watan Nuwamba 2018 aka karrama Moses Armah a kasar Canada saboda gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa kwallon kafa a yammacin Afrika.[10]
Ya jagoranci Medeama SC don doke Asante Kotoko don lashe Kofin FA na Ghana a shekarar 2015.[11] Hakan ya biyo bayan irin nasarar da aka samu a kan wannan bangaren Kotoko shekaru biyu da suka gabata.[12]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Medeama president Moses Armah receives top award in Canada" . GhanaSoccernet . 27 November 2018. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Find out how corrupt referees compelled team owner to sell the club – Ghana Sports Online" . 16 September 2019. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Premier League clubs submit names to vote at GFA Elective Congress" . www.ghanaweb.com . 2019-10-15. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Why Muntari slapped Moses Armah - Nyantakyi" . Graphic Online . Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Moses Armah 'Parker' finally opens up on Muntari feud" . www.ghanaweb.com . 2016-06-22. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Boateng, Muntari sent home, suspended 'indefinitely' by Ghana" . Eurosport . 2014-06-26. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Ex-Ghana coach Kwesi Appiah reveals Sulley Muntari bruises with blood after 2014 World Cup fight" . GhanaSoccernet . 4 February 2020. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ Association, Ghana Football. "Medeama drawn in Group A of CAF Confederations Cup" . www.ghanafa.org . Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Medeama SC through to play-off round of Caf Confederation Cup after 2-1 aggregate win over Zesco United | Goal.com" . www.goal.com . Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Medeama president Moses Armah receives top award in Canada" . GhanaSoccernet . 27 November 2018. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "FA Cup Final: Medeama beats Asante Kotoko 2-1" . www.ghanaweb.com . 2015-08-30. Retrieved 2020-07-07.
- ↑ "Medeama stun Kotoko to win FA Cup" . Pulse Gh . 2016-08-30. Retrieved 2020-07-07.