Moreto Cassamá
Moreto Moro Cassamá (an haife shi a ranar 16 ga watan Fabrairu, shekara ta 1998) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na Bissau-Guine wanda ke taka leda a Stade de Reims, wace ta ke a kasar faransa, a matsayin ɗan wasan tsakiya. Ya wakilci Portugal a matakin ƙarami, kafin ya koma Guinea-Bissau a babban mataki.
Moreto Cassamá | |||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Bisau, 16 ga Faburairu, 1998 (26 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Guinea-Bissau | ||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.65 m |
Aikin kulob/Ƙungiya
gyara sasheA ranar 16 ga watan Satumba, shekara ta 2017, Cassamá ya fara buga wasansa na farko tare da FC Porto B a wasan 2017-18 LigaPro da Nacional.[1] A ranar ƙarshe ta summer transfer window, 31 ga watan Janairu 2019, an canza shi zuwa ƙungiyar Faransa ta Stade de Reims tare da kwantiragin har zuwa lokacin rani na shekarar 2022.[2]
Ƙasashen Duniya
gyara sasheAn zabe shi ne a tawagar kwallon kafa ta Guinea-Bissau don gasar cin kofin Afrika na 2019 kuma ya fara buga wasansa na farko a duniya a wasan rukuni na karshe da Ghana a ranar 2 ga watan Yulin 2019, ya shigo a matsayin wanda zai maye gurbin Burá a minti na 64.[3]
Manazarta
gyara sasheHanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Moreto Cassamá at ForaDeJogo
- Moreto Cassamá at Soccerway
- Moreto Cassamá at National-Football-Teams.com