Monireh Gorji
Monireh Gorji malama ce a kasar iran kuma yar gwagwarmaya. ita kadai ce mace ta farko da aka fara zaba cikin kwararrun mutane guda 73 da zasu yi aiki akan kundin tsarin mulki na kasa a shekarar alif 1979. Su wannan kwararru su ke da alhakin zabe da kuma sa ido ga dukkan yadda shugaban kasa ke gudanar da ayyuka.[1]
Monireh Gorji | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tehran, 1930 (94/95 shekaru) |
ƙasa | Iran |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Jam'iyar siyasa | Islamic Republican Party (en) |
Ayyuka da gudunmuwar data bayar
gyara sasheAkwai rubuce rubuce daban daban daga masana akan ayyukan Gorji da gudunmuwar ta, misali a shekarar 1980 an ambaci aiyukan ta a mukala mai suna "Mata a tsarin mulkin musulunci na Iran". Sannan ta bada gudunmuwa wajen yada kare hakki da yancin mata a kasar Iran, inda ta kafa hujja da muhimmancin kare hakkin mata da kuma rawar da mata suke takawa daga mahangar littafin Al Kur'ani mai tsarki.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ervand Abrahamian (1989), "To The Masses", Radical Islam: the Iranian Mojahedin, Society and culture in the modern Middle East, vol. 3, I.B.Tauris, p. 195, Table 6, ISBN 9781850430773
- ↑ https://doi.org/10.1080%2F00210862.2012.726846