Mojisola Adekunle-Obasanjo (An haifeta 10 ga watan Agusta shekarar 1944 - 4 ga watan Yuni,shekarar 2009) mai ritaya ce daga cikin sojojin Najeriya da ta kafa jam'iyyar Gwagwarmayar Talakawa a Najeriya (Masses Movement of Nigeria) a shekarar 1998, daga baya ta yi takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Masses Movement of Nigeria (MMN) a shekarar 2003 . Ta Kuma yi takara a shekarar 2007 inda ta zama yar'takara mace kaɗai acikin waɗanda aka kaɗa wa ƙuri'a a matsayinta na mace ɗaya tilo da za ayi takara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2007 .]].[1][2]

Mojisola Adekunle-Obasanjo
Rayuwa
Haihuwa 10 ga Augusta, 1944
ƙasa Najeriya
Mutuwa Lagos, 4 ga Yuni, 2009
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Ta kasance tsohuwar matar aure (1991-1998) ta tsohon Shugaban ƙasan Najeriya Olusegun Obasanjo.[3]

Adekunle-Obasanjo ta mutu a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, shekarar 2009 a gidan 'yarta-Adetokunbo a birnin Ikoyi jihar Legas bayan gajeriyar rashin lafiya.[4][5]


Ta kasance ta bar tana da yara huɗu (4) da jikoki masu yawa.[5]

Aikin siyasa gyara sashe

Mojisola ta yi aiki a matsayin mai aikin gidan Rediyo tare da Sojojin Najeriya saboda mafi yawan ayyukanta kafin ta yi ritaya daga aiki. A shekarar 2003, Manjo Mojisola ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen shugaban ƙasa da na Gubernatorial. Ta samu adadin kuri'u 157,560 wanda ya yi daidai da 0.40% na ƙuri'un da aka amince da su.

Ta kuma yi takara a zaɓen Najeriya na shekarar 2007 kuma an kayar da ita.[6][7][8]

Manazarta gyara sashe

  1. James Ezema. "Women in Politics: Challenges, and the Rwandan Example". Newswatch Times. Archived from the original on April 22, 2015. Retrieved April 22, 2015.
  2. Celestine Okafor (April 3, 2004). "We'll mobilise the masses, says Moji Obasanjo!". Vanguard media. Retrieved April 22, 2014.
  3. Britannica (April 3, 2004). "Biography of Obasanjo!". Britannica website. Retrieved April 22, 2014.
  4. Godwin Mbachu (March 5, 2015). "Female Presidential Candidates: How Far can They Go?". Leadership News. Archived from the original on June 11, 2016. Retrieved April 22, 2015.
  5. 5.0 5.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Biography of Obasanjo Britannica
  6. All Africa. "Nigeria: Moji Obasanjo Dies at 65". AllAfrica.
  7. Gupta, K.R (2005). Studies in World Affairs, Vol. 1 (1 ed.). India: Atlantic Publishers & Distributors (P) Ltd. p. 116. ISBN 9788126904952.
  8. Sahara Reporters. "Major Moji Obasanjo is Dead!-PM News, Lagos". Sahara Reporters. Retrieved 11 March 2019.

Haɗin waje gyara sashe