Mohamed Qotb Abou Gabal Ali (Larabci: محمد قطب أبو جبل علي; an haife shi 29 ga Janairun shekarar 1989), wanda kuma aka fi sani da Gabaski, kwararren dan wasan kwallon kafa ne na kasar Masar wato Egypt wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida a kulob din Zamalek na Premier na Masar da kuma tawagar kasar Masar.[1]

Mohamed Abou Gabal
Rayuwa
Haihuwa Asyut (en) Fassara, 29 ga Janairu, 1989 (35 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
ENPPI Club (en) Fassara2010-2013
Zamalek SC (en) Fassara2013-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai tsaran raga
Tsayi 1.96 m
Imani
Addini Musulunci

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

Gabaski ya kasance cikin tawagar Masar don gasar Afcon 2021 (wanda aka gudanar a 2022). An kawo shi ne a matsayin wanda zai maye gurbinsa a karawar da Masar ta yi da Ivory Coast a zagaye na 16. Ya ceci bugun daga kai sai mai tsaron gida Eric Bailly, inda ya taimakawa Masar ta ci gaba. A wasan daf da na kusa da na karshe Gabaski ya fara wasan amma an sauya shi a cikin karin lokaci saboda raunin da ya samu a tsoka, duk da cewa kungiyarsa ta yi nasara a wasan. A wasan dab da na kusa da na karshe ya ceci bugun fanareti biyu daga Kamaru sannan ya taimakawa Masar ta kai wasan karshe. Bugu da kari, ya kuma ture fenaritin mane a wasan karshe na AFCON.[2]

Girmamawa gyara sashe

ENPPI

  • Kofin Masar: 2010–11

Zamalek

  • Gasar Premier ta Masar: 2014-15, 2020-21
  • Kofin Masar: 2014, 2015, 2018–19
  • Super Cup na Masar: 2019-20
  • CAF Super Cup: 2020

Manazarta gyara sashe

  1. "Mohamed AbouGabal - Player profile". Soccerway. Retrieved 27 February 2019.
  2. "Afcon 2021: Egypt XI to face Senegal - Salah, Elneny start, Ashour in for suspended Kamal | Goal.com". www.goal.com. Retrieved 2022-02-06.