Micah Yohanna Jiba ɗan siyasan Najeriya ne. Ya kasance memba a majalisar wakilai ta tarayya, mai wakiltar Abuja Municipal Area Council/Bwari Federal Constituency a majalisar wakilai. [1] Joshua Chinedu Obika ne ya gaje shi.

Micah Jiba
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Municipal/Bwari
Rayuwa
Haihuwa 1969 (55/56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwar farko

gyara sashe

An haifi Micah Jiba a shekara ta 1969. [1]

Aikin siyasa

gyara sashe

Jiba ya taɓa zama Kansila Garki Ward, kuma Shugaban Hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC). [2] A shekarar 2022, ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin ya tsaya takara a zaɓen majalisar wakilai na shekarar 2023. A ƙarshe ya samu nasarar doke abokan takararsa, Abuzarri Suleiman Ribadu na APC da Joshua Chinedu Obika na Labour Party (LP). [3] A watan Yunin 2023, ya kaddamar da ayyuka kusan 25 a sassa daban-daban na mazaɓar sa. [4] Ya yi Allah-wadai da rugujewar da aka yi wa unguwar Akpanjiya a birnin tarayya Abuja. [5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-12. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. Ng, Metro News (2022-05-23). "Hon Micah Jiba emerged PDP candidate". METRO DAILY Ng (in Turanci). Retrieved 2024-12-12.
  3. Yahaya, Hussein (2022-05-23). "PDP primaries: Jiba wins AMAC/Bwari fed constituency". Daily Trust. Retrieved 2024-12-12.
  4. Okah, Paul (2023-06-13). "AMAC/Bwari constituency: Jiba commissions 25 projects across communities". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2024-12-12.
  5. Abdulsalam, Kehinde (2020-08-16). "Lawmaker condemns demolition of FCT community". Daily Trust. Retrieved 2024-12-12.