Matthias N'Gartéri Mayadi
Matthias N'Gartéri Mayadi (1942 - ranar 19 ga watan Nuwamban a shekarar 2013) bishop ne na Roman Katolika na Chadi. Shi ne babban Bishop na Roman Katolika na Archdiocese na N'Djaména a Chadi daga shekarar 2003 har zuwa mutuwarsa a 2013. [1]
Matthias N'Gartéri Mayadi | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Cadi |
Suna | Matthias |
Shekarun haihuwa | 1942 da 1946 |
Wurin haihuwa | Mandoul Region (en) |
Lokacin mutuwa | 19 Nuwamba, 2013 |
Wurin mutuwa | Colombier-Saugnieu (en) |
Harsuna | Larabci da Faransanci |
Sana'a | Catholic priest (en) da Catholic bishop (en) |
Muƙamin da ya riƙe | Roman Catholic Archbishop of N'Djamena (en) , diocesan bishop (en) , diocesan bishop (en) , titular bishop (en) da auxiliary bishop (en) |
Addini | Cocin katolika |
Consecrator (en) | Paul Zoungrana, Charles Louis Joseph Vandame da Henri Véniat (en) |
An naɗa N'Gartéri Mayadi a matsayin firist a ranar 30 ga watan Disamban 1978 kuma ya zama bishop na Sarh a shekarar 1987, wanda ya kasance har zuwa shekarar 1990. Ya kasance bishop na Moundou daga shekarar 1990 zuwa 2003. A ranar 31 ga watan Yulin 2003, N'Gartéri Mayadi ya gaji Charles Louis Joseph Vandame a matsayin babban Bishop na N'Djaména.