Masawud Mohammed (an haife shi 1 Afrilu 1971), ɗan siyasa ne na ƙasar Ghana kuma ɗan majalissar na bakwai na jamhuriya ta huɗu ta Ghana mai wakiltar mazabar Pru ​​ta Yamma a yankin Bono ta Gabas a karkashin jam'iyyar National Democratic Congress.[1][2]

Masawud Mohammed
Member of the 7th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2017 -
District: Pru West Constituency (en) Fassara
Election: 2016 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 6th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017
District: Pru West Constituency (en) Fassara
Election: 2012 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 1 ga Afirilu, 1971 (53 shekaru)
ƙasa Ghana
Karatu
Makaranta University of Cape Coast Master of Education (en) Fassara : Ilimin halin dan Adam
University of Cape Coast Bachelor of Education (en) Fassara : Ilimin halin dan Adam
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da consultant (en) Fassara
Imani
Addini Musulmi
Jam'iyar siyasa National Democratic Congress (en) Fassara

Shekarun farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Mohammed a ranar 1, ga Afrilu 1971, a Prang a yankin Bono. Ya halarci Jami'ar Cape Coast kuma ya kammala karatun digiri da digiri na biyu a fannin Ilimi.[2][3]

Mohammed ya kasance dan majalisa mai wakiltar Pru ​​West Constituency. Kafin wannan aiki ya yi aiki a matsayin malami a Kwalejin Ilimi ta Atebubu sannan ya zama shugaban gundumar Pru.[2][3]

Ya fara zama dan majalisa a shekarar ta 2013, mai wakiltar mazabar Pru ​​West. A shekarar ta 2016, ya sake tsayawa takarar kujerar a babban zaben 2016, kuma ya yi nasara. Ya samu kuri'u 10,740. Wanda ke wakiltar kashi 49.66% , na yawan kuri'un da aka kada, don haka ya doke sauran 'yan takarar da suka hada da Stephen Pambiin Jalulah da Eric Kwabena Asamoah da Akurugu Zakarai Atiah.[2][4]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Mohammed musulmi ne. Yana da aure da ‘ya’ya hudu.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Hon. Masawud Mohammed". Parliament of Ghana. Retrieved 3 August 2020.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 "Ghana MPs - MP Details - Mohammed, Alhaji Masawud". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-02-01.
  3. 3.0 3.1 "Ghana Parliament member Masawud Mohammed (Alhaji)". www.ghanaweb.com. Retrieved 2020-02-01.[permanent dead link]
  4. FM, Peace. "Ghana Election 2016 Results - Pru West Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-02-01.