Masarautar Patigi Jiha ce ta gargajiya ta Najeriya wacce Idrissu Gana na ɗaya ya kafa ta a shekarar 1898, sunan patigi yana nufin ' karamin tudu ' Masarautar dake cikin ƙaramar hukumar pategi ta jihar kwara kuma babban birnin Pategi.[1]

Masarautar Pategi
Emirate (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1898
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaKwara
Mazaunin mutanePatigi (en) Fassara

Masarautar gyara sashe

Idrssu Gana ne ya kafa Masarautar wanda a shekarar 1898, ya jagoranci wata ƙungiya (Kede), wata ƙungiya ce ta ƴan ƙabilar Nupe daga Bida a yakin da Turawan Mulkin Mallaka suka yi, kuma mutanen Nupe da yare na Yarbawa ne ke zaune a masarautar. daga cikin mutanen akwai manoma masu fatauci da masunta.[ana buƙatar hujja]

Masarautar duka mutanen Nupe ne a cikinta kuma tana gudanar da bikin kwale-kwale da aka fi sani da Bikin Pategi Regatta wanda aka yi akasari a yankin kogin Neja a bakin Tekun Patigi. Taron kwale-kwale na tarihi da kuma yawon buɗe ido da Farfesa Idrissu Aliyu ya ce majalisar gargajiya ta Masarautar ne suka kafa ta a shekarar 1949 a hannun shugaban majalissar guda biyu, Ahman Pategi da Etsu Umaru Bologi I, an fara gudanar da bikin-ne a shekarar 1952, bakin kogin Niger Kwara da Niger Kogi. Bikin wanda ya ƙunshi tseren kwale-kwale ko kwale-kwale ya haɗa da baje kolin a Nijar Gbaradogi da ke gabar kogin yamma, Masarautar kuma ta yi bikin ranar al'adun Nupe da ake gudanarwa duk shekara a watan Yuli kuma ya kasance tarihin mamaye yankin Nupe gaba ɗaya kan Turawan mulkin mallaka.[2][3]

Jerin masu mulki gyara sashe

Sunan sarki a pategi ana kiransa da Etsu na Patigi. Etsu na Patigi na yanzu shine Alhaji Umar Bologi II.[4][5] Jerin sarakunan gargajiya na masarautar Patigi da aka fi sani da Etsu Patigi da aka kafa a ƙarni na 16:[6][7]

  • Etsu Idrissu Gana ɗan Muazu Isa I (b. 1856 - d. 1900). 1898-1900
  • Muazu Isa dan Idrissu Gana (b. 1882 - d. 1923). Nuwamba 1900 - 1923
  • Usman Tsadi dan Muazu Isa (d. 1931) 1923 -January 1931
  • Umaru dan Muazu Isa (b. 1898 - d. 1949) Janairu 1931 - 1949
  • Umaru Ibrahim Bologi 1st term (b.1939 - 2018) 1949 - 1966
  • Idrissu Gana II (b. 1933 - d. 1999) 26 Oktoba 1966 - 1999
  • Ibrahim Chatta Umar II (b. 1958 - 2019) 1999 - 2019
  • Umar Bologi II (an haife shi 1982) 2019 zuwa yau.

Manazarta gyara sashe

  1. Jimada, Idris Sha'aba. (2016). The historical background to the establishment of Patigi Emirate : c. 1810-1898. ISBN 978-978-54467-9-1. OCLC 1122566972.
  2. Apter, Andrew (2008-10-01). The Pan-African Nation: Oil and the Spectacle of Culture in Nigeria (in Turanci). University of Chicago Press. ISBN 978-0-226-02356-4.
  3. highprofile (2019-03-22). "IEDPU mourns Etsu Pategi". High Profile (in Turanci). Retrieved 2020-03-24.
  4. "INEC promises free, fair, credible by-election in Kwara". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-02-28. Retrieved 2020-03-24.
  5. Haour, Anne (2007-12-27), "Rulers", Rulers, Warriors, Traders, Clerics, British Academy, doi:10.5871/bacad/9780197264119.003.0003, ISBN 978-0-19-726411-9
  6. "Nigerian traditional polities". www.rulers.org. Retrieved 2020-03-24.
  7. "Nigerian Traditional States". www.worldstatesmen.org. Retrieved 2020-03-24.