Masarautar Jarin
Masarautar Jarin wata masarauta ce ta farko wacce take a arewa maso gabashin Afirka. A cewar Al-Yaqubi, daya ce daga cikin masarautun Beja guda shida da suka wanzu a yankin a karni na 9. Yankin masarautar tana tsakanin Gash-Barka da Massawa.[1] [2] Sarkin Jarin ya taso ne tun daga Massawa da ke gabar tekun Bahar Maliya, har zuwa iyakar Gash-Barka mai iyaka da masarautar Baqlin. Tana daya daga cikin masarautun Beja biyar da Al-Yaqubi ya lura da su.[3]
Masarautar Jarin | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 9 century | |||
Rushewa | 9 century |
Tarihi
gyara sasheA lokacin middle ages an kafa masarautun Beja guda biyar. Wadannan masarautu sun taso daga Eritrea zuwa Aswanin Masar. Masarautar Beja sun mamaye da yawa daga cikin tsohon yankin daular Axum. Wadannan masarautun dai sanannen malamin tarihi na Larabawa Al-Yaqubi ne ya fara bayyana su a karni na 9 miladiyya Sunayen masarautun su ne Naqis, Baqlin, Bazin, Jarin da Qat’a. Masarautun suna da iyaka da juna da kuma masarautar Nubian Alodia. A kudancin masarautun Beja akwai daular kiristoci da ake kira Najashi. An samu zinariya, duwatsu masu daraja da emeralds a yawancin masarautu. Al-Yaqubi ya lura cewa Larabawa musulmi sun ziyarci masarautun ne domin kasuwanci. Ya kuma lura cewa Larabawa suna aiki a ma'adinan gwamnati. [4] Babban ayyukan kasuwanci na masarautun Beja sune hakar ma'adinai da cinikin bayi. An kafa wata muhimmiyar cibiyar cinikin bayi a tsibirin Dahlak. An yi cinikin bayi daga cikin Afirka zuwa yankin Larabawa da sauran su. A tsakiyar mulkin Beja, yawancin zuriyar daular Axum ko dai an kore su daga yankin ko kuma an sayar da su a matsayin bayi.[5]
Garuruwan da ke cikin masarautar Jarin sun hada da Suakin da Aydhab. Duk da haka, garuruwan biyu sun kasance masu zaman kansu daga harkokin siyasa kuma suna ƙarƙashin kariya ta Masar.
Duba kuma
gyara sashe- Sultanate of Ifat
- Adal Sultanate
- Masarautar Bazin
- Masarautar Belgium
- Masarautar Nagash
- Masarautar Qita'a
- Masarautar Tanki
Manazarta
gyara sashe- ↑ Yaʻqūbī, Aḥmad ibn Abī Yaʻqūb,? (2018). The Works of Ibn Wāḍiḥ al-Yaʻqūbı̄ : an English translation . Leiden. ISBN 9789004364165 .
- ↑ Elzein, Intisar Soghayroun (2004). Islamic Archaeology in the Sudan . Archaeopress. p. 13. ISBN 1841716391 . Retrieved 3 March 2015.
- ↑ Yaʻqūbī, Aḥmad ibn Abī Yaʻqūb,? (2018). The Works of Ibn Wāḍiḥ al-Yaʻqūbı̄ : an English translation . Leiden. ISBN 9789004364165 .
- ↑ Yaʻqūbī, Aḥmad ibn Abī Yaʻqūb,? (2018). The Works of Ibn Wāḍiḥ al-Yaʻqūbı̄i : an English translation . Leiden. ISBN 9789004364165 .
- ↑ Tronvoll, Kjetil (1998). Mai Weini, a highland village in Eritrea : a study of the people, their livelihood, and land tenure during times of turbulence . Lawrenceville, NJ: Red Sea Press. ISBN 9781569020586 .