Masarautar Bazin
Masarautar Bazin wata masarauta ce ta farko wacce take a arewa maso gabashin Afirka. A cewar Al-Yaqubi, tana ɗaya daga cikin gwamnatocin Beja guda shida da suka wanzu a yankin a karni na 9. Yankin masarautar yana tsakanin Aswan da Massawa.[1]
Masarautar Bazin | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 9 century | |||
Rushewa | 9 century |
Yawancin jama'ar 'yan asalin Kunama ne, da ake kira "Bazin" (ko wani lokacin Baden, Bazen da dai sauransu), waɗanda suke yin addinin gargajiya. Mutanen Bazin sun kasance karkashin kariyar daular Abyssiniya.[2] An bayyana wannan a cikin abin da ake kira Dutsen Ezana, inda aka ce wani Sarkin Aksumite da ba a bayyana sunansa ba ya kare Bazin daga mamaye Noba. Da rugujewar Masarautar Aksum a kusan shekara ta 700 AD, dangin Beja sun mamaye kuma suka kafa masarautu da dama a Eritrea ta yau, ciki har da Bazin.
Duba kuma
gyara sashe- Sultanate of Ifat
- Adal Sultanate
- Masarautar Belgium
- Masarautar Jarin
- Masarautar Nagash
- Masarautar Qita'a
- Masarautar Tanki