Masallacin Omar Ibn Al-Khattab
Masallacin Omar Ibn Al-Khattab ( fassarar Spaniyanci Omar Iban Al-Jattab ) masallaci ne a Maicao, La Guajira, a Kasar Colombia. Shi ne masallaci na uku mafi girma a Latin Amurka. Ana kiran shi kuma da "La Mezquita" ("Masallacin"), saboda shine masallaci tak a yankin. Tare da Makarantar Dar Alarkan, su ne cibiyoyin addinin Musulunci da al'adunsu a yankin. An gina masallacin a ranar 17 ga watan Satumban 1997, kuma an sa masa suna bayan halifan Sunni na biyu Omar Ibn Al-Khattab .[1] Masanin gine-ginen na kasar Iran Ali Namazi ne ya zana masallacin, wanda injiniyan gine-gine Oswaldo Vizcaino Fontalvo ya gina, ta amfani da marmara ta Italiya don gina ta. Zai iya ɗaukar mutane aƙalla sama da mutum dubu ɗaya.
Masallacin Omar Ibn Al-Khattab | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Kolombiya |
Department of Colombia (en) | La Guajira Department (en) |
Municipality of Colombia (en) | Maicao (en) |
Coordinates | 11°22′41″N 72°14′04″W / 11.3781°N 72.2344°W |
History and use | |
Opening | 1997 |
Ƙaddamarwa | 17 Satumba 1997 |
Suna saboda | Sayyadina Umar |
Addini | Musulunci |
Suna | Sayyadina Umar |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | Islamic architecture (en) |
Tsawo | 31 m |
Offical website | |
|
Cikin Masallacin
gyara sasheA bakin kofar akwai babban zaure wanda aka kawata shi da rubutun larabci. Bugu da kari, akwai wani zauren, wanda ya fi na farkon girma, inda maza ke sallah. Anan ne ma suke haduwa domin kawo karshen lokutan azumi. Soron wannan ɗakin yana da zane-zane na ado. Daga gabas akwai wurin da mata suke sallah, wanda ke sama da wurin ibada na maza. Saman masallacin zagaye yake da hasumiyoyi.
A kasan manyan matakalan fita daga masallacin akwai daƙin da ake yiwa mamaci wanka kafin a kai gawar zuwa makabartar Musulman yankin.
Duba kuma
gyara sashe- Jerin masallatai a Amurka
- Jerin masallatai
- Musulunci a Kolombiya
Manazarta
gyara sashe- ↑ "La Mezquita Omar Ibn Al Khattab, 10 años ligada a la historia de Maicao" [The Mosque of Omar Ibn Al-Khattab, 10 years linked to the history of Maicao]. El Informador (in Spanish). 17 September 2007. Archived from the original on 3 March 2016. Retrieved 27 October 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)