Margot Parker
Margaret Lucille Jeanne Parker (an haife ta a ranar 24 Yuli 1943) yar siyasa ce ta Turai wacce ta yi aiki a matsayin memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) a yankin Gabashin Midlands tsakanin 2014 da 2019. An haife ta a Grantham kuma ta yi karatu a Kesteven da Grantham Girls School da kuma Jami'ar De Montfort, inda ta karanta Law.
Margot Parker | |||||
---|---|---|---|---|---|
15 ga Afirilu, 2019 - 1 ga Yuli, 2019 District: East Midlands (en)
1 ga Yuli, 2014 - 14 ga Afirilu, 2019 District: East Midlands (en) Election: 2014 European Parliament election (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Grantham (en) , 24 ga Yuli, 1943 (81 shekaru) | ||||
ƙasa | Birtaniya | ||||
Harshen uwa | Turanci | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
De Montfort University (en) Kesteven and Grantham Girls' School (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | UK Independence Party (en) | ||||
margotparkermep.uk |
Parker ta tsaya takarar Libertas a zaben 2009 na Turai a Gabashin Midlands . Ita ce ta biyu a jerin jam’iyyar; jam'iyyar ta samu kashi 0.6% na kuri'un da aka kada kuma babu kujeru.
Ta koma UK Independence Party (UKIP) a shekara na gaba. Ta tsaya a Sherwood a babban zabe na 2010, inda ta kammala 5th (kiri'u 1,490, 3%). A cikin 2012, ta tsaya a zaben Corby, ta zo na uku da kuri'u 5,108 (14.3%).
A shekara ta 2014, an zaɓi Parker a matsayin ɗan takara na biyu akan jerin Gabas ta Tsakiya don UKIP a shirye-shiryen zaben majalisar Turai na 2014. Daga baya an zabe ta tare da Roger Helmer a matsayin MEP na UKIP na yankin Gabashin Midlands.
Bayan zaben Henry Bolton a matsayin shugaban UKIP a 2017, an nada Parker mataimakin shugaba. Baya da Bolton ya ki Amin cewa da aniyar ajiye takara bayan kuri’ar rashin amincewa da kwamitin zartarwa na UKIP ya yi, Parker ta yi murabus a matsayin mataimakiyar shugaba.
A lokacin shugabancin Gerard Batten, Parker ta yi aiki a matsayin mai magana da yawu a harkokin cikin gida kuma mataimakiyar shugabar jam'iyyar Independence Party ta Burtaniya, amma ta yi murabus daga mukaminta da zama memba na jam'iyyar a watan Afrilun 2019, ta koma jam’iyyar Brexit Party, tare da Jane Collins & Jill Seymour, tana ambaton karewar Batten na Carl Benjamin ta tweet na 2016 yana mai cewa "ba zai ma yi fyade ba" dan majalisar Labour Jess Phillips .
Duk da sauya shekar ta, an ki zabi Parker a matsayin 'yar takarar jam'iyyar Brexit ba don zaben majalisar Turai na 2019, kuma ta daina Neman matsayin memba na Majalisar Tarayyar Turai a ranar 26 ga Mayu 2019.