Manjo Janar Farouk Yahaya (An kuma haifeshi a shekara ta alif dari tara da sittin da shida 1966) a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya.

Aikin soja gyara sashe

Ya shiga aikin soja a shekara ta alif dari tara da tamanin da biyar 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na shekarar alif dari tara da casa'in 1990. Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka:- Laftana - ranar 27 ga Satumba shekarar alif dari tara da casa'in 1990 Kyaftin - ranar 27 ga watan Satumba na shekarar alif dari tara da casa'in da huɗu 1994 Manjo - ranar 27 ga watan Satumba na shekarar alif dari tara da casa'in da takwas 1998. Laftanar Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2003. Kanar - ranar 27 ga watan Satumban shekarar 2008 Birgediya Janar - ranar 27 ga watan Satumba 2013 Manjo Janar - ranar 27 ga watan Satumba 2017. [1]

Hafsan soji gyara sashe

Sabon babban hafsan sojin kasan na Najeriya ya yi karatun digirinsa na farko a fannin Tarihi sannan ya yi digiri na biyu wato Masters a kan harkokin siyasar kasashen duniya da difilomasiyya. Ya rike mukamai daban-daban ciki har da mataimakin sakataren rundunar soji da kuma sakataren na rundunar soji a hedikwatar sojin ƙasa. Mukamin da ya rike na karshe kafin naɗin nasa shi na jagorantar yaƙi da Boko Haram karkashin rundunar Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya. [2]

Kwamanda gyara sashe

Ya taɓa kuma riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko wato General Officer Commanding (GOC) 1 Division. Kafin nadinsa a mukamin General Officer Commanding 1 Division, Manjo Janar Yahaya ya kuma jagoranci runduna ta 4 da ke hedikwatar rundunar sojin Najeriya. Kazalika ya rike mukamin Kwamandan rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, a jihar Borno. [3] A shekarar 2019, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jagoranci rundunar Operation CLEAN SWEEP wadda ta fatattaki 'yan bindigar da ke dajin Kuduru a Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Yanzu shine babban Hafsan Sojojin Najeriya.

Manazarta gyara sashe