Mahuta

mazaɓa a jihar Katsina, Najeriya

Mahuta dai gari ne mai matukar tasiri da yawan al'umma a karamar hukumar Dandume a jihar Katsina. Garin Mahuta gari ne dake gabashin garin Dandume wadda ita ce hedikwatar karamar hukumar. Mahuta na da ward wato Mazabu uku (3), Mahuta A, Mahuta B da kuma Mahuta C. Garin mahuta shi ne gari mafi girman Gaske bayan cikim garin Dandume a wannan hukumar ta DandumeAn kirkiri garin na mahuta a shekarar (1909).

Mahuta

Wuri
Map
 11°26′30″N 7°16′00″E / 11.4417°N 7.2666°E / 11.4417; 7.2666
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Katsina
BirniKatsina
mahuta

Mutanen garin Mahuta suna noma da kasuwanci dai dai gwargwadon iko. Bugu da kari Kuma mutanen na garin suna kokari wajen neman illimi musamman na boko da na addini kuma Allah madaukakin sarki ya albarkaci 'ya'yansu da kwakwalwa da basirar fahimtar karatu. Bangaren karatun addini ma ba abarsu abaya ba kuma akwai makarantun allo wadanda basa kirguwa, banda zaurukan karatuttuka da masallatai, akwai islamiyoyi da dama na bangaren izala da kuma darika. Bangaren karatun xamani ma ba'a barsu a baya ba inda suke da firamare har guda biyar ga kuma sakandire babba da karama. Akwai 'yan secondary, masu N.C.E, Diploma, Degree, Masters, PhD har da ma Farfesa duk a cikin garin Mahuta. Dan majalisar jiha Mai wakiltar karamar hukumar Dandume Alh. Yahaiya Nihu Dan Mahuta ne. Vice Chancellor na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua ta Katsina Dan Mahuta ne.

Tarihi gyara sashe

Garin mahuta dai Dadadden gari ne da ya samo asali sama da shekaru casa'in (90), kuma a wancan lokacin garin ya shahara wajen kasuwanci a yankin, inda garin ke da babbar kasuwar da take tasiri a yankin gaba daya tare da hamshakan manoma a garin dama yankin baki ɗaya.

Manazarta gyara sashe