Mahmud Mohammed
Mahmud Mohammed, CON, OFR (an haife shi 10 Nuwamba shekara ta alif ɗari tara da arba'in da shida1946A.c). masanin shari'a ne dan Najeriya kuma tsohon Alkalin Alkalan Najeriya.[1][2][3]
Mahmud Mohammed | |||
---|---|---|---|
2014 - 2016 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jalingo, 10 Nuwamba, 1946 (78 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | mai shari'a |
Kuruciya
gyara sasheAn haifi Mai shari'a Mohammed a ranar 10 ga watan Nuwamba 1946.,a Jalingo babban birnin jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya.[4] Ya sami digiri na farko a fannin shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello a shekarar 1970, kuma aka kira shi zuwa kungiyar lauyoyin Najeriya, a shekarar da ya kammala makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya.[5]
Aikin shari'a
gyara sasheYa shiga aikin shari’a a lokacin tsohuwar jihar Arewa maso Gabas a matsayin lauya, kuma a shekarar 1991, ya zama babban alkalin alkalan jihar Taraba, a shekarar ne aka tabbatar da nadinsa a matsayin babban alkalin jihar.[6] A 2005, an nada shi mai shari'a a Kotun Koli ta Najeriya.[7] A watan Nuwamba 2014, an nada shi a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya ya gaji Aloma Mariam Mukhtar, mace ta farko a Najeriya.[8] Mai shari'a Mahmud Mohammed shine shugaban majalisar shari'a ta kasa.[4]
Kungiyoyi
gyara sashe- Memba, Kungiyar Lauyoyin Najeriya
- Memba, gungiyar Lauyoyin Duniya
- Memba, Kungiyar Benchers ta Najeriya
- Memba, Majalisar Shari'a ta Kasa
Manazarta
gyara sashe- ↑ "TVC NEWS - Justice Mahmud Mohammed - Magistrate judges - Nigeria - TVC NEWS". tvcnews.tv. Retrieved 28 April 2015.
- ↑ "CJN warns judges against scuttling 2015 polls". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 28 April 2015. Retrieved 28 April 2015. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "Jonathan, others honour fallen heroes". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 25 June 2015. Retrieved 28 April 2015. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ 4.0 4.1 "FJSC Nominates Mahmud Mohammed as Next CJN, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Retrieved 28 April 2015.
- ↑ "Justice Mahmud Mohammed". Vanguard News. Retrieved 28 April 2015.
- ↑ "Jonathan approves Justice Mahmud Mohammed as next CJN". DailyPost Nigeria. Retrieved 28 April 2015.
- ↑ OUR REPORTER. "The man Justice Mahmud Mohammed". The Nation. Retrieved 28 April2015.
- ↑ "Mahmud Mohammed: The new Chief Justice of Nigeria". Daily Independent, Nigerian Newspaper. Retrieved 28 April 2015.