Louis Stedman-Bryce
Louis Stedman-Bryce (an haife shi a watan Disamban shekarar 1974) darektan gida ne na Biritaniya, mai sanya hannun jari a kadarori kuma tsohon ɗan siyasa. Ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) a Scotland tsakanin shekarata 2019 zuwa 2020. An zabe shi a matsayin dan takarar jam'iyyar Brexit amma ya bar jam'iyyar a watan Nuwamba 2019 ya tsaya matsayin mai zaman kansa.
Louis Stedman-Bryce | |||
---|---|---|---|
2 ga Yuli, 2019 - 31 ga Janairu, 2020 ← Catherine Stihler (en) District: Scotland (en) Election: 2019 European Parliament election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Kent (en) , Disamba 1974 (49 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Leeds (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Brexit Party (en) |
Kuruciya da aiki
gyara sasheAn haifi Stedman-Bryce a watan Disamba 1974 ga mahaifi dan Jamaica da kuma mahaifiya 'yar Birtaniya kuma ya girma a Kent, Ingila, kafin ya koma Scotland.[1] [2] Ya kasance daraktan gida kuma dan kasuwa, shi ne wanda ya kafa iNkfish Capital kuma darektan kula da iNkfish Care da ci gaban kadarorin iNkfish.[3][1][4]
Siyasa
gyara sasheA matsayinsa na dan takarar jam'iyyar Brexit, Sedman-Bryce an zabe shi a matsayin dan majalisar Turai na yankin Scotland a zaben majalisar Turai na shekarar 2019 kuma ya hau kujerarsa a ranar 2 ga Yuli 2019, ya zama dan majalisa baki na farko da aka zaba a Scotland.[5][6][7] A wani bangare na jam'iyyar, ya ce ba zai taba shiga jam'iyyar Independence Party ta Burtaniya ba kuma yana son jam'iyyar Brexit ta zama "coci mai fadi".[8]
Stedman-Bryce ya kasance dan takarar majalisar wakilai na jam'iyyarsa (PPC) na Glasgow North East a babban zaɓen 2019 . Sai dai kuma ya tsaya tsayin daka domin nuna adawa da matakin da Nigel Farage ya dauka na kin tsayawa takara a kujeran da Conservative ke rike da ita. Stedman-Bryce ya yi iƙirarin wannan yana ba Boris Johnson damar isar da wata matsala ta hanyar janye yarjejeniyar Brexit.[9]
Kwanaki bayan tsayawa takara a matsayin dan takara a zaɓen duka gari, Sedman-Bryce ya bar jam’iyyar Brexit gaba daya ya zauna a matsayin MEP mai cin gashin kansa bayan ya dauki batun tsarin tantance ‘yan takarar jam’iyyar.[10] Ya kasance MEP har zuwa ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai a ranar 31 ga Janairu 2020.[11]
A lokacin zamansa a Majalisar Turai, Stedman-Bryce ya kasance na shida a cikin jerin 'Yan majalisa da suka fi kowa samun kudi a jam'iyyar Brexit a bayan Nigel Farage wanda ya kasance na biyar.[12] Shi ne bakar fata na farko kuma daya tilo da ya taba wakiltar Burtaniya a Majalisar Tarayyar Turai.[13]
Rayuwa
gyara sasheStedman-Bryce ya kasance ɗan luwaɗi a bayyane kuma ya auri abokin kasuwancinsa Gavin.[14][15]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Louis STEDMAN-BRYCE – Personal Appointments (free information from Companies House)". beta.companieshouse.gov.uk. Retrieved 28 March 2020.
- ↑ "Boothman, John (19 May 2019). "'We are not selfish, right-wing or homophobic' says Louis Stedman-Bryce, Brexit Party candidate in European elections in Scotland". Retrieved 27 May 2019 – via www.thetimes.co.uk.
- ↑ "McLaughlin, Mark (17 May 2019). "Louis Stedman-Bryce: Brexit Party 'would not stand in way' of independence vote". Retrieved 27 May 2019 – via www.thetimes.co.uk.
- ↑ Halliday, Josh (25 April 2019). "Brexit party: opera singer and ex-Loaded editor on candidate list". Retrieved 27 May 2019 – via www.theguardian.com.
- ↑ "The UK's European elections 2019". BBC News. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ "Key dates ahead". European Parliament. 20 May 2017. Archived from the original on 25 May 2019. Retrieved 28 May 2019.
- ↑ "Key dates ahead". BBC News. 22 May 2017. Retrieved 28 May 2019.
- ↑ "People don't trust politicians': Louis Stedman-Bryce on why he supports a no deal Brexit". Holyrood Website. 4 November 2019. Retrieved 28 March 2020.
- ↑ "Scottish Brexit Party MEP with 'heavy heart' stands down in protest". www.scotsman.com. 13 November 2019. Retrieved 15 November 2019.
- ↑ "MEP Louis Stedman-Bryce resigns from Brexit Party". Holyrood Website. 19 November 2019.
- ↑ Barnes, Peter (5 February 2020). "What happens after Brexit?". BBC News. Retrieved 28 March 2020.
- ↑ These are all the highest-earning Brexit Party MEPs". Scram News. 27 September 2019. Retrieved 18 July 2020.
- ↑ "The Brexit Party's only Scottish MEP just quit over party's selection of candidate who 'declared war' on LGBT community". PinkNews - Gay news, reviews and comment from the world's most read lesbian, gay, bisexual, and trans news service. 19 November 2019. Retrieved 5 August 2020.
- ↑ "Gay Brexit Party candidate: 'We're not all homophobic racists' · PinkNews". www.pinknews.co.uk. 25 April 2019. Retrieved 27 May 2019.
- ↑ "Clarke, Sarah (15 April 2019). "Scottish entrepreneurs launch live-in care service, creating 100 jobs". Home Care Insight. Retrieved 15 November 2019.