Libianca Fonji
Libianca Kenzonkinboum Fonji, wadda aka sani da sunan Libianca.An haife ta a 2000 ko 2001, mawaƙiyar Afrobeats ce. Kuma yar ƙasar Kamaru ce. Ta yi gasa a cikin kaka na ashirin da ɗaya na nunin gidan talabijin na Amurka <i id="mwEQ">The Voice</i> a cikin 2021. An fi saninta da waƙar " People " 2022, wanda aka yi ma wahayi daga cyclothymia . Waƙar ta yi karo na 2 akan ginshiƙi na Billboard Afrobeats na Amurka kuma ta sami karɓuwa a kafafen sada zumunta da dama.
Libianca Fonji | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Minneapolis (mul) , 2001 (22/23 shekaru) |
ƙasa |
Tarayyar Amurka Kameru |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi |
Artistic movement |
Afrobeats contemporary R&B (en) Afro-soul (en) |
Jadawalin Kiɗa | RCA Records (mul) |
IMDb | nm13064073 |