Lawrence Nomanyagbon Anini (c. 1960 – Maris 29, 1987) [1] Dan fashi ne a Najeriya wanda yayi aiyukan ta'addancin sa a birnin Benin na Najeriya a shekarun 1980 tare da na hannun daman sa Monday Osunfor. An kamashi kuma an rataye shi sakamakon aikin tada kayar baya da yayi.

Lawrence Anini
Rayuwa
Haihuwa 1960
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1987
Yanayin mutuwa  (gunshot wound (en) Fassara)
Sana'a
Sana'a bank robber (en) Fassara

An haifi Anini a wani kauye kusa da birnin Benin wanda yake a jihar Edo a yanzu. Tun yana da kananun shekaru yayi kaura inda ya koma birnin Benin, anan ya koyi tuki kuma yazamo direban motar Taksi. Yayi suna sosai a tashar motar Benin saboda yadda ya kware wajen iya sarrafa mota. Ya fara da tuka boyayyun tsagerun a birnin inda daga bisani kuma ya sauya zuwa tuka gungun yan fashi da masu tayar da kayar baya da dukkan masu aiyukan ta'addanci, inda suka kware wajen tare hanya da fasa banki. A hankali ya kara fadada aiyukan ta'addancin sa zuwa sassa da dama na arewaci da gabashin Benin.


An kama Anini a ranar 3 ga Disamba, 1986, a wani gida a birnin Benin ta hanyar hadin baki da budurwar sa. An harbi Anini a kafa inda akayi ta kaishi asibitin sojoji domin kulawa da lafiyar sa inda daga bisani kuma saidai aka yanke kafar.[2] Jagorancin gwamnatin soja ta Ibrahim Babangida, ta bukaci ayi wani gwaji. A karshe dai an tabbatar da zarge zargen laifukan da akema Anini da dama inda aka yanke masa hukuncin rataya ranar 29 ga Maris, 1987.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 P E Igbinovia (Spring 1988). "Wound Ballistics, Reasonable Force and Anini's Incapacitation". International Journal of Comparative and Applied Criminal Justice. 12 (1): 131–135. doi:10.1080/01924036.1988.9688886. Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2020-05-03.
  2. Film of the execution broadcast by BBS TV Benin Channel 55
  • Marenin, Otwin (June 1987). "The Anini Saga: Armed Robbery and the Reproduction of Ideology in Nigeria". The Journal of Modern African Studies. 25 (2): 259–281. doi:10.1017/S0022278X00000380. JSTOR 161014.