Stefani Joanne Angelina Germanotta lafazi|ˈstɛfəni_ˌdʒɜːrməˈnɒtə (An haife ta a watan Maris 28, shekarar 1986), anfi saninta da Lady Gaga, Mawaƙiyar kasar Tarayyar Amurka ce, Marubiciyar waka, kuma jaruma. An santa da sauya yanayin halitta da salo iri-iri. Gaga ta fara waka tun tana budurwa a tsakanin shekaru 13 zuwa 19, Tana yin wake a dararen open mic da yin wasannin a shirye-shiryen makaranta. Ta yi karatu a Collaborative Arts Project 21, ta Jami'ar New York Tisch School of the Arts, sannan daga bisani ta fita dan ci gaba da sana'ar wake-wake. Bayan Def Jam Recordings sun soke kontaraginta, sai ta fara aiki a matsayin marubuciyar waka wa Sony/ATV Music Publishing, inda kada hannu a sabon yarjeniya da Interscope Records da kuma KonLive Distribution a cikin shekara ta 2007. Gaga ta kuma samu daukaka a shekara mai zuwa bayan ta fitar da album dinta na farko The Fame, da kuma wakokin dai dai da suka haye jadawali, "Just Dance" da kuma "Poker Face". An kuma sake faɗaɗa albam din kuma an sanya EP, The Fame Monster (2009), da sabbin wakoki kamar su "Bad Romance", "Telephone" da "Alejandro", kuma duk sun sami karbuwa.
[[Grammy Award for Album of the Year(en) ]] (2011) : [[Born This Way(mul) ]] [[Grammy Award for Best Pop Vocal Album(en) ]] (2011) : [[Born This Way(mul) ]] [[American Music Award for Favorite Pop/Rock Album(en) ]] (2011) : [[Born This Way(mul) ]] [[Juno Award for International Album of the Year(en) ]] (2012) : [[Born This Way(mul) ]] [[Academy Award for Best Original Song(en) ]] (14 ga Janairu, 2016) : [[Til It Happens to You(en) ]] [[Academy Award for Best Original Song(en) ]] (22 ga Janairu, 2019) : [[Shallow]] [[Academy Award for Best Actress(en) ]] (22 ga Janairu, 2019) : [[A Star Is Born(en) ]] [[Grammy Award for Best Pop Vocal Album(en) ]] (2021) : [[Chromatica]] [[Grammy Award for Best Pop Duo/Group Performance(en) ]] (2021) : [[Rain on Me]] [[Academy Award for Best Original Song(en) ]] (24 ga Janairu, 2023) : [[Hold My Hand]]