Labaran Maku
Labaran Maku (an haife shi a shekara ta 1962) shi ne tsohon Ministan Watsa Labarai a Nijeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015. Ya fito daga jihar Nassarawa.
Labaran Maku | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Satumba 2013 - ga Maris, 2014
11 ga Yuli, 2011 - 29 Mayu 2015 ← Dora Akunyili
Mayu 2003 - Mayu 2007
Mayu 2003 - Mayu 2007 | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | 1 ga Janairu, 1962 (62 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Jami'ar, Jos | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Grand Alliance |
Farkon rayuwa da Karatu
gyara sasheAn haifi Maku ne a ranar 1 ga watan Janairun shekara ta alif dari tara da sittin da biyu 1962 a Gundumar Wakama a Nassarawa Eggon Local Govt Area na Jihar Nassarawa kuma yana da aure da ’ya’ya.
Ya halarci Makarantar Firamare ta St Michael, Aloce tsakanin shekarar 1970-1976, Kwalejin Koyarwar Zawan, Bukuru-Jos, Jihar Filato, 1976-1981 da Jami'ar Jos ta Jihar Filato 1983–1987. Maku ya fara siyasa da shugabanci tun yana karami kuma ya rike mukamin Shugaban kungiyar daliban Jami’ar Jos da PRO na Kungiyar Kasa ta Daliban Najeriyar NANS, a lokacin da yake makaranta.
Ayyuka da Siyasa
gyara sasheYana da digiri na farko a Tarihi / Ilimi kuma ya halarci shirye-shiryen horo da yawa, Taron Kasashen Duniya, taruka da Shugabannin Kasashe. Ya gabatar da Takardu a Taron Kasa da Kasa, ya kasance Babban Bako a taruka na Shugabanci da dama kuma ya yi rubuce-rubuce da yawa a kan ilimin Najeriya da rashin daidaito a tsakanin al’umma da kuma matsalolin siyasa da tattalin arzikin Najeriya. Ya yi aiki tare da USAID daga shekarar 1997 - 1999. Ya kasance mai rahoto, Editan Siyasa, memba na Hukumar Edita ta Jaridun Kasa biyu kuma Mataimakin Babban Edita a lokacin aikinsa na Jarida. Ya kuma yi aiki a matsayin Malamin makaranta da Shugaban makaranta a makarantun gwamnati daga shekarar 1981 - 1983.
Ya kasance Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa daga shekara ta 2003 zuwa 2007, inda ya dauki nauyin jagoranci na Hukumomin Hukumomi da Cibiyoyi. Kafin wannan, ya kasance Kwamishinan Yada Labarai na Matasa da Wasanni 1999–2002, da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida 2002–2003. Ya kasance mai magana da yawun Jiha kuma jigo a fagen tsara manufofin Jiha.
Ya zama karamin Ministan Yada Labarai da Sadarwa a watan Yunin shekarar 2010 sannan daga baya ya hau kujerar Ministan Yaɗa Labarai da Sadarwa a watan Disambar 2010. Ya yi murabus ne a ranar 20 ga Oktoba, 2014 don cigaba da burinsa na takarar gwamna a 2015 a Jihar Nasarawa. [1]