Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Fasaha) Bichi

Technical College of Education in Kano State

Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Fasaha), Bichi babbar makarantar gwamnatin tarayya ce da ke Bichi, Jihar Kano, Najeriya . Tana da alaƙa da Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa don karatun digiri. Shugaban makarantar na yanzu shi ne Bashir Muhammad Fagge.[1]

Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Fasaha) Bichi

Bayanai
Iri school of education (en) Fassara da jami'a
Ƙasa Najeriya
Harshen amfani Turanci
Tarihi
Ƙirƙira 1986
fcetbichi.edu.ng

An kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Fasaha), Bichi a shekarar 1986.[2]

Cibiyar tana ba da darussa kamar haka;[3]

  • Ilimin Kula da Yara na Farko
  • Tarihi Tarihi
  • Nazarin Addinin Kirista
  • Ilimi na Musamman
  • Ilimin Fasaha
  • Ilimin Kwamfuta
  • Larabci
  • Ilimin Manya da Na Zamani
  • Ilimin Kimiyya
  • Kimiyyar Noma
  • Ilimin Halitta
  • Ilimin Lantarki/Electronics
  • Karatun Ilimin Firamare
  • Tattalin Arzikin Gida
  • Ilimin Fasahar Gina
  • Ilimin Fasahar Ƙarfe
  • Ilimi da Haɗakar Kimiyya
  • Faransanci
  • Ilimin Jiki Da Lafiya
  • Ilimi da Lissafi
  • Fine And Applied Arts
  • Ilimin Kasuwanci

Cibiyar tana da alaƙa da Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa don bayar da shirye-shiryen da za su kai ga samun digiri na ilimi, (B.Ed.) a;[4]

  • Ilimin Lantarki/Electronics
  • Ilimin Fasahar Gina
  • Ilimin Fasahar Aikin ƙarfuna

Manazarta

gyara sashe
  1. "The Provost – Federal College of Education (Technical) Bichi" (in Turanci). Archived from the original on 2021-08-13. Retrieved 2021-08-13.
  2. "Schools | FCE(T) Bichi". www.fcetbichi.edu.ng. Archived from the original on 2021-08-13. Retrieved 2021-08-13.
  3. "Official List of Courses Offered in Federal College Of Education (Techinical) Bichi (FCETBICHI) - Myschool". myschool.ng (in Turanci). Retrieved 2021-08-13.
  4. "List of Degree Courses Offered in Federal College of Education (Technical), Bichi (FCETBICHI)". Academia Nigeria (in Turanci). 2018-05-01. Archived from the original on 2021-08-13. Retrieved 2021-08-13.