Kwadwo Mama Adams
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Kwadwo Mama Adams 'dan siyasa ce dan kasar Ghana kuma dan majalisa ta biyu a jamhuriya ta hudu mai wakiltar mazabar Techiman ta kudu a yankin Brong Ahafo na kasar Ghana.[1][2]
Kwadwo Mama Adams | |||
---|---|---|---|
7 ga Janairu, 1997 - 6 ga Janairu, 2001 District: Techiman South Constituency (en) Election: 1996 Ghanaian general election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Yankin Brong-Ahafo, | ||
ƙasa | Ghana | ||
Mutuwa | 7 Satumba 2002 | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | National Democratic Congress (en) |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Adams a Techiman ta Kudu a yankin Brong Ahafo na Ghana.[3]
Siyasa
gyara sasheAn fara zaben Adams a matsayin dan majalisa kan tikitin jam'iyyar National Democratic Congress a lokacin babban zaben Ghana na mazabar Techiman ta kudu a watan Disamban shekarar 1996. Ya samu kuri'u 24,164 ɗaga cikin sahihin kuri'u 39,698 da aka kada wanda ke wakiltar kashi 46.30% akan Jarvis Reginald Agyeman-Badu na New Patriotic Party wanda ya samu kuri'u 15,534 da ke wakiltar 29.80%.[4]
Sana'a
gyara sasheBaya ga kasancewarsa tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Techiman ta kudu. Ya kasance mataimakin ministan yankin Brong Ahafo.[5]
Mutuwa
gyara sasheAdams dai ya rasu ne a wani hatsarin mota a lokacin da motar da yake tukawa daga Accra zuwa Sunyani ta yi hatsari da wata motar tipper a kusa da Suhum. An kai gawarsa Asibitin Koyarwa na Korle-Bu domin a duba lafiyarsa. Ya rasu ranar 7 ga Satumban, shekarar 2002.[6][7][8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ghanaian Parliamentary Register(1993–1996)
- ↑ "Ode To The NDC (2) - Ghanamma.com" (in Turanci). Retrieved 9 October 2020.
- ↑ Ghanaian Parliamentary Register(1993–1996)
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 1996 Results – Techiman South Constituency". Ghana Elections – Peace FM. Retrieved 9 October 2020.
- ↑ Ghanaian Parliamentary Register(1993–1996)
- ↑ "NDC Chairman Dead". Modern Ghana. Retrieved 9 October 2020.
- ↑ "NDC Chairman Dead". www.ghanaweb.com. 8 September 2002. Retrieved 9 October 2020.
- ↑ Ghanaian Parliamentary Register(1993–1996)