Kisan kiyashin Kebbi, Maris 2022

Kisan gilla a Najeriya

A ranar 8 ga Maris, 2022, wasu gungun ‘ yan bindiga sun kashe mutane sama da 80 a jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya.

Infotaula d'esdevenimentKisan kiyashin Kebbi, Maris 2022
Iri harin ta'addanci
Bangare na Ƴan ƙungiyar fashi a Najeriya
Kwanan watan 8 ga Maris, 2022
Wuri Jahar Kebbi
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 80
Adadin waɗanda suka samu raunuka 8
yan bindigan Najeriya

Matashiya

gyara sashe

Rikicin ‘yan fashin Najeriya ya faro ne a shekarar 2011. Yana faruwa ne a yankin arewa maso yammacin Najeriya, tsakanin kungiyoyin da ke ɗauke da makamai da gwamnati, waɗanda bayan shekaru goma aka ayyana ƙungiyoyin a matsayin 'yan ta'adda . Kungiyoyin VNSA sukan kai hare-hare kan gwamnati da fararen hula, ciki har da harbe-harbe da kuma yin garkuwa da jama'a . Mummunan harin da ‘yan ƙungiyar suka kai shi ne kisan gillar da aka yi a Zamfara a shekarar 2022 . Hare-haren da suka kai a jihar Kebbi sun haɗa da kisan kiyashi da garkuwa da mutane, duka a watan Yunin 2021, da kuma kisan kiyashi a watan Janairun 2022.

harbe-harbe

gyara sashe

A ranar 8 ga Maris, 2022 a garin Sabaka, ‘yan bindiga sun yi wa ƴan banga (ƴan Sa Kai) kwanton bauna suka kashe mutane 62 daga cikin ƴan bangar a Kebbi.[1][2]

Da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar ne wasu gungun ‘yan bindiga suka shiga wani matsugunin kogi kusa da Kanya, Wasagu/Danko . Suka bar baburansu a baya suka kewaye Kanya. Maharan sun shiga garin Kanya inda suka yi wa tawagar mataimakin gwamnan kwanton bauna inda suka kashe sojoji goma sha uku da ‘yan sanda biyar da kuma ɗan banga.[3] Wasu mutane takwas kuma sun jikkata.[2]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kashe-kashen.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. Muhammad, Garba (2022-03-08). "Gunmen kill at least 62 vigilantes in Nigeria's Kebbi state". Reuters (in Turanci). Retrieved 2022-03-11.
  2. 2.0 2.1 Reuters (2022-03-10). "Gunmen kill 19 soldiers in attack on Nigerian deputy governor's convoy". Reuters (in Turanci). Retrieved 2022-03-11.
  3. "Gunmen in Northwest Nigeria Kill 19 Security Personnel". VOA (in Turanci). Retrieved 2022-03-11.
  4. "Kebbi massacre shocking, security forces must do more - Buhari - P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2022-03-11.