Kisan kiyashi a Kebbi, 2021
(an turo daga 2021 Kisan kiyashin Kebbi)
A ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2021, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyuka takwas a jihar Kebbi, arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kashe akalla mutane 90.
Iri | harin ta'addanci |
---|---|
Kwanan watan | 3 ga Yuni, 2021 |
Wuri | Jahar Kebbi |
Ƙasa | Najeriya |
Adadin waɗanda suka rasu | 90 |
Faruwar Lamarin
gyara sasheAn fara kai harin ne da karfe 3 na rana; ‘ Yan bindigar da suka hau babura sun kai farmaki kauyukan Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da kuma Iguenge.[1][2] ‘Yan bindigar sun fito ne daga jihohin Niger da Zamfara da ke makwabtaka da Najeriya, sun kuma yi awon gaba da shanu tare da lalata amfanin gona.[1][3][4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Attackers kill 88 people in northwestern Nigeria edition.cnn.com
- ↑ "Gunmen attack villages, kill over 90 in Nigeria". DW. Retrieved 27 June 2021.
- ↑ "Bandits kill 88 in Kebbi". guardian.ng. 5 June 2021.
- ↑ "Cattle thieves kill 88 in northwest Nigeria massacre". www.theweek.in.