Kisan kiyashi a Yelwa

Rikicin addini tsakanin Musulmi da Kirista a Yelwa, Najeriya a shekara ta 2004.

Kisan kiyashin Yelwa: dai ya kasance jerin tashe-tashen hankula masu nasaba da addini tsakanin Musulmi da Kiristoci wanda ya faru a Yelwa, Najeriya tsakanin watan Fabrairu zuwa Mayun 2004. Waɗannan al'amura sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 700. [1] Na farko ya faru ne a ranar hudu (4) ga watan Fabrairun 2004 lokacin da wasu ɓaragurbin Musulmai ɗauke da makamai suka kai wa Kiristocin Yelwa hari, inda suka kashe Kiristoci fiye da 78, ciki har da aƙalla 48 da ke ibada a cikin harabar coci. [1] A cewar wasu majiyoyi, alamar harin na kiran jihadi ne daga masallacin yankin. [2]

Infotaula d'esdevenimentKisan kiyashi a Yelwa
Iri Kisan Kiyashi
Kwanan watan 2004
Wuri Jahar pilato
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 1,000

Kisan da aka yi a watan Fabrairu ya ƙara ruruta wutar rikici tsakanin al’ummomin da ke ƙara ta’azzara tun Rikicin Jos, 2001 lokacin da rikici tsakanin Musulmi da Kiristocin ya yi sanadin mutuwar mutane 1,000. A ranar 2 ga Mayu, 2004 Kiristocin yankin sun mayar da martani game da abin da ya faru a watan Fabrairu ta hanyar kai wa Musulmai hari a Yelwa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kusan 630.[1] Wasu majiyoyi sun ce an tilasta wa ’yan mata musulmi cin naman alade da sauran abincin da aka haramta wa musulmi, har ma an yi musu fyaɗe.[2]

Wai-wa-ye

gyara sashe

Dubban mutane ne suka mutu a faɗa tun bayan amincewar shari'ar Musulunci a yankin arewacin ƙasar da musulmi ke da rinjaye bayan komawar mulkin farar hula a shekarar 1999. [3] Asalin rikicin Kirista Tarok da fulani musulmi ya samo asali ne daga ikirari da suke yi kan filayen noman jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya. [4]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 "Revenge in the Name of Religion", Human Rights Watch, 26 May 2005.
  2. 2.0 2.1 "God's Country", The Atlantic March 2008.
  3. BBC profile of Nigeria. BBC News (16 May 2013).
  4. "Nigerian Muslims struggle to cope after village massacre", The Guardian (8 May 2004).

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe