Kirikiri Babban Gidan Kurkuku da Tsaro

Kurkuku mafi girman tsaro na Kirikiri gidan kurkuku ne da ke a yammacin garin Apapa, a jihar Legas, Najeriya. Dalilin kiranta da wannan suna saboda tana ƙauyen Kirikiri. Wani ɓangare ne na Hukumar Kula da Gyaran Halayya, a Najeriya. Yawan adadin Fursunoni da gidan ke iya dauka a hukumance sune fursuna 1,056. An fara kafa ta a shekarar 1955. Paul Chiama na gidan jaridar Leadership ya rubuta cewa "Ambaton Kirikiri ya fara tunatar da duk wani dan Najeriya" wannan gidan yari.

Kirikiri Babban Gidan Kurkuku da Tsaro
Wuri
Coordinates 6°26′40″N 3°18′28″E / 6.44433°N 3.307904°E / 6.44433; 3.307904
Map

Tun daga ranar 1 ga watan Fabrairu shekarar, 1990 Tana ɗaukar Fursunoni 956 amma a zahiri tana ɗaukar fursunoni 1,645. Wani rahoto na 1995 da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kanada ta yi ya bayyana cewa “gidan yarin ta riga ta yi suna” saboda cunkoso da take dashi.[1] A watan Maris din shekarar 2018 ne Ƙasar Birtaniya ta sanar da cewa za ta kashe dalar Amurka $939,000 don gina wani sabon reshe mai gadaje 112, domin a samu sauƙin kwashe fursunonin Najeriya daga Birtaniya. duk da cewa babu wani rahoto ya bayyana cewa Gwamnatin Burtaniya tayi wannan aikin.

Akwai wasu fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa a Kirikiri.[2]

An gina gidan yarin na Kirikiri a shekara ta 1955 tare da fursunoni 1056 na farko. Ya zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu, shekarar 2018, kashi 69% cikin ɗari na Fursunonin dake a gidan yarin suna jiran shari’a ne kamar yadda bayanai daga hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta tabbatar.

Har zuwa watan Oktoba shekarar 2021 a gidan yarin Kirikiri (Gidan Dan Kanden Kirikir), a da ana ciyar da fursunoni abinci na Naira 450 a rana (kimanin dalar Amurka 1.08 kamar a watan Mayu shekarar 2022). A cikin watan Oktoban 2021 Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Cikin Gida ya kara yawan abincin yau da kullun zuwa Naira 1,000 (kimanin $2.41 kamar a watan Mayu 2022). Jami’an hukumar gyaran Hali ta Najeriya sun bayar da shawarar a ba su alawus na naira 750 a kullum, sai dai kwamitin majalisar dattijai sunce wannan adadin bai isa ba. A cikin wata hira da gidan jaridar Vanguard tayi da wani Fursuna a watan Mayun 2022, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa abincin da ake ci a Kirikiri "dan kadan wanda baya isar koda karamin yaro ballatan babban mutum, kuma abicin baida kyau sam". Misali, yace shi wnada ba'a bayyana sunan sa ba, karin kumallon Gidan Yarin ya ƙunshi wake da aka dafa shi kaɗai ba ko magi, kowace safiya, tsawon kwana bakwai a mako. Fursunonan da ba a bayyana sunansa ba ya kuma kwatanta karuwar tallafin abinci na yau da kullun wanda ake ikirarin ana badawa a matsayin "Zancen kanzon kurege", yana mai cewa, "Idan har kana bukatar sanin haka to ku zo ku gani da Idonku, don sanin ainihin abin da nake gaya a kai" kuma" ku zo ku ga abinci mai ban tsoro! Abin har yayi muni.”

Wani fursuna da aka yi fira da shi wanda gidan jaridar Vanguard tayi da shi a watan Mayu sekarar 2002 ya bayyana cewa "ko da mayunwacin kare ba zai ci abincin da suke ba mu ba", kuma wasu fursunoni sun dogara da samun damar dafa abinci a ɗakin su don su rayuwa. Ana iya siyan danyen abincin da fursunoni za su dafa a cikin dakunansu ta hannun jami’an kula da walwala na gidan yarin, kuma wasu fursunoni suna da garwar kalanzir da Risho don su girka abincinsu. Wani fursuna ya bayyana cewa gidan yarin yana da wani “sashen VIP” daban, inda fursunonin ke da nasu mai dafa abinci, da mai wanke tufafi, masu aiki da kuma na’urar samar da wutar lantarki.

A watan Mayun shekarar 2022, mai magana da yawun hukumar gidajen yari ta jihar Legas, ya musanta ikirarin cewa har yanzu fursunonin na karbar abinci naira 450 ne kawai a kowace rana, yana mai cewa, “an yi nazari kan ciyarwar kamar yadda aka bayyana a cikin dokar kula da gidajen yari ta Najeriya na shekarar 2019. N450 na farko an duba shi sama amma na tabbata bai kai sama da N1000 ba. Dole ne in gaya muku cewa game da ciyarwa a gidajen yari, akwai ma'auni guda ɗaya da muke amfani da shi don kowane rabon abinci ga fursunoni." Sabanin wannan bayani, wani babban jami’in gidan yarin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa “babu wani abu da ya canza dangane da ciyar da fursunoni a fadin kasar nan” kuma “babu wani abu da ya canza a nan ta fuskar inganci da yawan abincin da fursunonin ke ci. Har yanzu ita ce masifa da wahala ta yau da kullum na abincin Ẹ̀bà tare da miya egusi mai ruwa, wake da shinkafa." Babban jami'in ya kuma bayyana cewa "Hanya daya tilo da fursunonin ke rayuwa ita ce ta hanyar samar da nasu abincin."

Sanannun fursunoni

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "Nigeria: Information on Kirikiri Maximum Security Prison, the type of prisoners kept there, on the structure of the prison, and on the treatment of prisoners". refworld.org. Retrieved 3 July 2023.
  2. Whitehead, Eleanor. "Nigeria's addiction to the death sentence." Al Jazeera. August 11, 2015. Retrieved on July 3, 2023.