Kingsley Kuku an haife shi a ranar 14 ga Fabrairu, 1970 ɗan Najeriya ne mai fafutukar kare haƙƙin muhalli da siyasa, mashawarci na musamman ga tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan na Najeriya kan harkokin Neja Delta kuma shugaban shirin afuwa na shugaban ƙasa.

A zamaninsa na jami'a, ya taba zama dan gwagwarmayar dalibai, shugaban dalibai kuma wani jami'in hada kai na kungiyar daliban Najeriya na kasa. Ya shiga fafutukar ganin an dawo da mulkin dimokradiyya a Najeriya. Ya ci gaba da kasancewa majagaba a ci gaba da maido da zaman lafiya mai dorewa a yankin Neja-Delta na Najeriya.

Kingsley Kuku bayan shigarsa da matasan kabilar Ijaw ya tsaya takara aka zabe shi a matsayin dan majalisar dokokin jihar Ondo sannan ya zama shugaban kwamitin majalisar na tsawon shekaru hudu. An nada shi a matsayin mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara a shekarar 2011. A wannan shekarar ya kasance bako mai jawabi a Chatham House, cibiyar kula da harkokin kasa da kasa, inda ya gabatar da takarda. Ya samu kyaututtukan karramawa da dama a birnin Atlanta na kasar Amurka.

Manazarta

gyara sashe

[1] [2] [3]

  1. NAN-H-105. "Presidency Sends Fund Request to Nass for Amnesty Programme, Others". News Agency of Nigeria. Archived from the original on 9 January 2014. Retrieved 17 April 2012.
  2. Newswire (19 December 2011). "Budget: NSA to spend N124bn, as amnesty gets N74bn". ASABA POST.
  3. Dan Onwukwe. "4 years of Amnesty in N/Delta: The pains, the gains". Sun Newspaper. Archived from the original on 24 June 2013. Retrieved 24 June 2013.