Khuraira Musa
Khuraira Musa Ƴar Najeriya ce, mazauniyar Amurka, ita shahararriyar kuma kwararriyar mai-kwalliya ce, shafe-shafe da kuma taimakon al'umma,[1] itace wacce ta zama shugaba ce ta kamfanin Khuraira kayan kwalliya. Khuraira ta shahara a fagen kwalliya da shafe-shafe na duniya, wanda kuma ta kasance tana gudanar da ajujuwan koyarwa ga mutane daga duniya baki daya. A rayuwar ta tayi kwalliya ga shahararrun mutane kamar su, Brandy, Mandy Moore, Paula Abdul, Kirstie Alley, Natalie Cole, Cher, Suzanne Douglas, Trista Rehn da kuma Dr. Suzanne Rice.[2]
Khuraira Musa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Lere, |
Sana'a | |
Sana'a | masu kirkira da ɗan kasuwa |
Farkon rayuwa da aiki
gyara sasheKhuraira Musa an kuma haife ta a Ƙaramar hukumar Lere Jihar Kaduna, Najeriya. Ta rasa mahaifiyar ta a lokacin haihuwar ta, wanda hakan ne yasa ta rayu a gidan rainon marayu dake yankin Rukuba/Bassa a Jihar Plateau, amma bayan nan ta koma jihar Kaduna har sai da ta kammala makarantar sakandare.[1] A shekarar 1992 taje kwaleji a Tarayyar Amurka wanda anan ne ta fara aiki a shaguna. [3][2]
Ta kuma fara harkan kwalliya a shekarar 2004 sannan tayi shekara 23 a kan wannan harka na kwalliya[4]
Aikin agaji
gyara sasheKhuraira Musa ta kafa gidauniyar da ake kira da suna Arewa Development Support Initiative (ADSI) hukuma wacce bata gwamnati ba, da niyyar taimakawa cigaban matasa da mata a yankin Arewacin Najeriya.[5][6][7] Gidauniyar na tallafawa da samun karatu ga mata, sana'o'in hannu da dabarun kasuwanci. Khuraira itace ta samar da makarantar Zainab Memorial saboda karantar da marasa karfi musamman marayu waɗanda ke a Bassa/Rukuba a Jihar Plateau.[8][9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Khuraira Cosmetics. "Our founder Khuraira Musa". Archived from the original on 14 February 2019. Retrieved 16 September 2019.
- ↑ 2.0 2.1 "The Beauty of Giving Back to Society". Africa Newspage. 16 May 2016. Retrieved 16 September 2019.[permanent dead link]
- ↑ Bella Naija. "Introducing US based International Make-up Artist". Retrieved 16 September 2019.[permanent dead link]
- ↑ https://www.africannewspage.net/2016/05/khuraira-musa-beauty-business-giving-back-society/
- ↑ "NGO Urges Northerners To Return Lost Glory". Daily Trust. Retrieved 16 September 2019.[permanent dead link]
- ↑ "Dalilin Dana Kafa Masana'antar Kwalliya Da Shafe-Shafe". Daily Trust. Retrieved 16 September 2019.[permanent dead link]
- ↑ "Arewa Groups moves to alleviate porverty". Blueprint Newspaper. Retrieved 16 September 2019.
- ↑ "Women for women networking". North Jersey. Retrieved 16 September 2019.[permanent dead link]
- ↑ "Beauty of Entrpreneurship and the Joy of Giving Back". Blueprint Nigeria. Retrieved 16 September 2018.