Kandia Camara
Kandia Camara (an haife ta a ranar 17 ga watan Yuni 1959) Malama ce kuma 'yar siyasa 'yar ƙasar Ivory Coast wacce ita ce Shugabar Majalisar Dattijan Ivory Coast tun a ranar 12 ga watan Oktoba 2023.[1][2] Ita ce tsohuwar ministar harkokin waje a gwamnatin shugaba Alassane Ouattara.
Kandia Camara | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
6 ga Afirilu, 2021 - 18 Oktoba 2023 ← Ally Coulibaly (en)
| |||||||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Abidjan, 17 ga Yuni, 1959 (65 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa | Ivory Coast | ||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||
Makaranta | Jami'ar Félix Houphouët-Boigny | ||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa, education minister (en) , deputy (en) da foreign minister (en) | ||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||||||
Jam'iyar siyasa | Rally of the Republicans (en) |
ƙwararriyar 'yar wasan ƙwallon hannu ce kuma tana cikin ƙungiyar ASC Bouaké da ta lashe Kofin Zakarun Kulob na Afirka a shekara ta 1981.[3][4]
Ilimi da aiki
gyara sasheCamara ta sami digiri a fannin Ingilishi a Jami'ar Abidjan sannan ta sami shaidar ci gaba a fannin ilimi daga Jami'ar Lancaster da ke Ingila. Camara kwararriyar 'yar wasan ƙwallon hannu ce kuma zakarar Cote d'Ivoire sau biyu a shekarun 1974 da 1980 kuma ta lashe Kofin Zakarun Kulob na Afirka a shekara ta 1981 tare da ASC Bouaké.[5] Daga shekarun 1983 zuwa 1986, ta koyar da harshen Turanci a Kwalejin Zamani, de Cocody da kuma Kwalejin Treich-la-Plène.[6][7] Ta yi aiki a matsayin ƙwararriyar Malamar harshen Ingilishi a makarantar ƙwararrun otal ta Abidjan daga shekarun 1986 zuwa 2002. Ta kasance memba a ofishin ƙasa na Ƙungiyar Malamai ta Sakandare ta Cote d'Ivoire (SYNESCI) daga shekarun 1987 zuwa 1991 kuma memba na Ƙungiyar Malaman Mata na Afirka ta Faransa daga shekarun 1989 zuwa 1991. Ta kasance sakatare-janar na ofishin na ƙasa na Union des femmes du PDCI (UFPDCI) kuma mashawarciya ƙaramar hukuma a zauren garin Cocody tsakanin shekarun 1990 zuwa 1994. A cikin shekara ta 1994, ta zama Sakatare-Janar na Rassemblement des Femmes Républicaines (RFR) har zuwa shekara ta 1998 lokacin da ta karɓi ofishin shugaban kungiyar na ƙasa kafin ta yi murabus a watan Mayu 2006.[8]
Camara ta zama mataimakiyar magajin garin Abobo a shekara ta 2001 kuma ta yi aiki a wannan ofishin har zuwa shekara ta 2003, lokacin da aka naɗa ta mai ba da shawara ta musamman ga firaministan gwamnatin sasantawa da mika mulki ta ƙasa har zuwa shekarar 2010. A shekarar 2014 aka naɗa ta ministar ilimi ta ƙasa.[9]
Ta yi ministar harkokin waje a gwamnatin Achi I da gwamnatin Achi II.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Côte d'Ivoire - Senate". IPU.[permanent dead link]
- ↑ "Former Ivorian Foreign Minister Kandia Camara elected President of Senate". WADR. 13 October 2023.
- ↑ "Exclusif /Dossier-Biographie-Côte d'Ivoire : Parcours et cursus /Tout savoir sur les membres du nouveau gouvernement de la 3ème republique | AbidjanTV.net" (in Turanci). 2017-01-12. Retrieved 2021-03-09.
- ↑ "Henriette Diabaté, présidente, Kandia Camara SG: les femmes prennent le pouvoir au RDR". Abidjan.net. Retrieved 2021-03-09.
- ↑ "KandiaCAMARA (Ministre de l'Education Nationale, de l'Enseignement Technique et de la Formation Professionnelle ) - Abidjan.net Qui est Qui". Abidjan.net. Archived from the original on 2020-01-11. Retrieved 2021-03-09.
- ↑ "Dix choses à savoir sur Kandia Camara, ministre ivoirienne de l'Éducation nationale – Jeune Afrique". JeuneAfrique.com (in Faransanci). 2018-03-22. Retrieved 2021-03-09.
- ↑ "Côte d'Ivoire : la liste du nouveau gouvernement dévoilée – Jeune Afrique". JeuneAfrique.com (in Faransanci). 2017-01-11. Retrieved 2021-03-09.
- ↑ "Projet École fermée, mais cahiers ouverts: Kandia Camara dévoile comment vont se dérouler les cours à distance | FratMat". www.fratmat.info. Retrieved 2021-03-09.
- ↑ "COVID-19 en milieu scolaire: La Ministre Kandia Camara annonce la reprise de la sensibilisation "zero cas" | FratMat". www.fratmat.info. Retrieved 2021-03-09.