Jumoke Akindele
Jumoke Akindele lauya ce a Najeriya kuma mace ta farko da ta fara zama kakakin majalisar dokokin jihar Ondo. Hon. Bamidele Oleyelogun ne ya gaje ta.[1]
Jumoke Akindele | |||
---|---|---|---|
27 Mayu 2015 - 19 ga Maris, 2017 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Ondo, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Obafemi Awolowo | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifeta a Okitipupa, wani gari a jihar Ondo kudu maso yammacin Najeriya. Ta yi karatun firamare a St. John's Primary School a Okitipupa kafin ta ci gaba zuwa makarantar sakandaren ƴan mata ta St. Louis, Ondo inda ta sami takardar shaidar makarantar Afirka ta Yamma a 1981. Ta samu digiri na farko a fannin shari’a a jami’ar Obafemi Awolowo University, Ile Ife kuma ta yi aikin lauya na wasu shekaru kafin ta tsunduma cikin siyasa a shekarar 2006.
Harkar siyasa
gyara sasheA watan Afrilun 2007, ta yi takarar kujerar Mazaɓar, mazabar Okitipupa II amma ta sha kaye a hannun jam’iyyar adawa. Ta sake tsayawa takara ne a ranar 11 ga Afrilun 2011, kuma an zabe ta a matsayin ‘yar majalisar dokokin jihar Ondo, inda ta yi aiki a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisar kan Ilimi kafin a zabe ta a matsayin Shugaban Majalisar. A ranar 27 ga Mayu, 2015, aka zabe ta a matsayin Shugaban Majalisar sakamakon rasuwar tsohon kakakin Samuel Adesina. Ta bar mukamin shugabancin gidan ne a cikin takardar murabus mai kwanan wata 20 Maris 2018. Jumoke Akindele ita ce mace ta farko da ta fara zama kakakin majalisar a jihar.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Kayode Alfred. "Jumoke Akindele calls the shots in Ondo Assembly". The Nation.