Jules Olivier Koundé ( French pronunciation: ​ ʒyl ɔlivje kunde] ; an haife shi ne a ranar 12 ga watan Nuwamba a shekarata 1998) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne dan asalin kasar Faransa wanda ke taka leda a matsayin ɗan baya na tsakiya ko kuma na dama ga ƙungiyar kwallon kafa ta La Liga wato Barcelona da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Faransa .

Jules Koundé
Rayuwa
Cikakken suna Jules Olivier Koundé
Haihuwa Faris, 12 Nuwamba, 1998 (25 shekaru)
ƙasa Faransa
Benin
Harshen uwa Faransanci
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  FC Girondins de Bordeaux (en) Fassara2017-2019
  Sevilla FC3 ga Yuli, 2019-27 ga Augusta, 2022
  FC Barcelona27 ga Augusta, 2022-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Nauyi 70 kg
Tsayi 180 cm

Aikin kungiya gyara sashe

Bordeaux gyara sashe

 
Koundé tare da Bordeaux a cikin 2018

Koundé ya fara buga wasa na farko ne a kungiyar kwallon kafa ta Bordeaux a gasar Coupe de France a inda suka sha kaye na ci 2-1 a waje da US Granville a zagaye na 64 a ranar 7 ga Janairu 2018, yabuga duka cikakkun mintuna 90 na lokacin al'ada da cikakken mintuna 30 na karin lokaci. Ya fara wasansa na farko a gasar Ligue 1 a Bordeaux a wasan da suka doke Troyes da ci 1-0 mai ban hausi a ranar 13 ga watan Janairu na shekarar 2018. A ranar 10 ga watan ne Fabrairu 2018, Koundé ya zura kwallonsa ta farko a wasan da suka doke Amiens da ci 3-2 a gida. ita ce kwallonsa ta farko a gasar Ligue 1 da kuma kwallonsa ta farko da ya ci wa kungiyar ta Bordeaux.

Sevilla gyara sashe

A ranar 3 ga watan Yuli,na shekarar 2019, ya rattaba hannu a kungiyar kwallon kafa ta Sevilla wanda suke a kasar andalus. An bayar da rahoton kuɗin canja wurin da aka biya zuwa Bordeaux a matsayin € 25 miliyan. A kakar wasansa ta farko a Sevilla, ya taimaka wa kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA Europa a tarihinta na karo na shida kuma ya kasance cikin tawagar da ta fi fice a gasar.

Barcelona gyara sashe

A ranar 29 ga watan Yuli a shekarar 2022, kungiyar ta Barcelona ta ba da sanarwar yarjejeniya da Sevilla don canja wurin Koundé. Koundé bai buga wasan farko da Barcelona ta yi da Rayo Vallecano a gasar La Liga ba saboda kungiyar basu kai ga yi masa rajista ba saboda sun wuce iyakar albashin gasar. Haka kuma bai buga wasa na biyu da Barcelona ta yi da Real Sociedad ba a ranar 21 ga watan Agusta saboda wannan dalili. anyiwa Kounde rajista tare da La Liga ne a ranar 26 ga Agusta kuma ya fara halarta a hukumance a kungiyar kwanaki biyu bayan nasarar 4-0 a kan Real Valladolid a Camp Nou .

Hotuna gyara sashe

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Koundé rabin dan kasar Benin ne kuma rabin dan kasar Faransa.

Kididdigar sana'a gyara sashe

Kungiya gyara sashe

Appearances and goals by club, season and competition
Club Season League National cup League cup Europe Other Total
Division Apps Goals Apps Goals Apps Goals Apps Goals Apps Goals Apps Goals
Bordeaux 2017–18 Ligue 1 18 2 1 0 0 0 0 0 19 2
2018–19 Ligue 1 37 0 1 0 3 0 10[lower-alpha 1] 2 51 2
Total 55 2 2 0 3 0 10 2 70 4
DD 2019–20 La Liga 29 1 2 1 9Cite error: Invalid <ref> tag; refs with no name must have content 0 40 2
2020–21 La Liga 34 2 7 1 7[lower-alpha 2] 1 1[lower-alpha 3] 0 49 4
2021–22 La Liga 32 2 3 1 9[lower-alpha 4] 0 44 3
Total 95 5 12 3 25 1 1 0 133 9
Barcelona 2022–23 La Liga 16 0 3 0 5[lower-alpha 5] 0 2[lower-alpha 6] 0 26 0
Career total 166 7 17 3 3 0 40 3 3 0 229 13
Fitowa da burin tawagar ƙasa da shekara
Tawagar kasa Shekara Aikace-aikace Manufa
Faransa 2021 7 0
2022 11 0
Jimlar 18 0

Girmamawa gyara sashe

Sevilla

  • UEFA Europa League : 2019-20

Barcelona

  • Supercopa de España : 2022-23

Faransa

  • UEFA Nations League : 2020-21
  • FIFA ta zo na biyu a gasar cin kofin duniya : 2022

Mutum

  • UEFA Europa League Squad of the Season: 2019–20
  • La Liga Team of the Season: 2021–22

Manazarta gyara sashe


Cite error: <ref> tags exist for a group named "lower-alpha", but no corresponding <references group="lower-alpha"/> tag was found