Joel Ngandu Kayamba (an haife shi a ranar 17 ga watan Afrilun shekarar alif dari tara da casa'in da biyu miladiyya 1992) Dan wasan Kungiyar Kwallon kafa ne dan kasar Kongo a halin yanzu yana taka leda a Samsunspor a cikin TFF First League a aro daga Viktoria Plzeň.

Joel Ngandu Kayamba
Rayuwa
Haihuwa Kinshasa, 17 ga Afirilu, 1992 (32 shekaru)
ƙasa Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
FK Pardubice (en) Fassara2015-2017
  SFC Opava (en) Fassara2017-2018
FC Viktoria Plzeň (en) Fassara2018-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Joel Ngandu Kayamba Shi dan wasan kwallon kafa ne

Aikin kulob/Kungiya

gyara sashe

Farkon aikin a Jamhuriyar Czech

gyara sashe

Ya buga wasansa na farko a gasar Kwararru a Pardubice 's Czech National Football League sun tashi 1–1 a České Budějovice a ranar 6 ga watan Nuwamba a shekara ta 2015. Ya sanya hannu kan Opava a cikin watan yuli a shekara ta 2017.[1] A cikin farkon kakarsa tare da Opava, ya sami ci gaba zuwa babban matakin kwallon kafa na Czech, Czech First League.[2] Ya kuma lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na watan a waccan kakar.[3] Ya zura kwallon da ya ci nasara a gasar farko ta Czech Opava-nasara da ci 2–0 a gida da Jablonec a ranar 1 ga watan Satumba a shekara ta 2018.[4]

Viktoria Plzeň

gyara sashe
 
Joel Ngandu Kayamba

A watan Satumba na shekara ta 2018, Kayamba ya rattaba hannu kan kwangila tare da FC Viktoria Plzeň akan farashin canja wuri na € 800,000. Shugaban Opava Marek Hájek ya bayyana cewa wannan motsi ya ƙunshi rikodin canja wurin kudaden shiga ga kulob din, ya karya rikodin da ya gabata wanda shine sayar da Libor Kozák.[5] Kayamba kuma zai ci gaba da zama a Opava a matsayin aro har zuwa ƙarshen shekarar 2018.[6]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Ya buga wasansa na farko a kungiyar kwallon kafa ta DR Congo a ranar 17 ga watan Nuwamba a shekara ta 2020 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da Angola. Ya maye gurbin Jordan Botaka a minti na 80.[7]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Ya koma Jamhuriyar Czech daga Faransa a shekara ta 2013, ya auri mata ’yar Czech kuma yana da ‘ya’ya biyu. Yana magana da yaruka hudu sosai: Faransanci, Ingilishi, Czech da Lingala.[8]

Manazarta

gyara sashe
  1. Kayamba míří do Opavy. Má i na první ligu, tuší v Pardubicích". iDNES.cz. 20 June 2017. Retrieved 2 September 2018.
  2. Udrží Opava opory pro ligu? Kayambu či Kuzmanoviče láká Olomouc- iSport.cz". iSport.cz. Retrieved 2 September 2018.
  3. Hráč měsíce Kayamba: Přezdívku Mireček jsem přijal, díky fanouškům jsem nahoře. Nabídky z ligy odmítl". FORTUNA:NÁRODNÍ LIGA. Retrieved 2 September 2018.
  4. Seznam.cz. "Opava poprvé v sezóně vyhrála" (in Czech). Retrieved 2 September 2018.
  5. Joel Kayamba míří do Plzně, jde o největší přestup Opavy". Opavský a hlučínský deník (in Czech). 6 September 2018. Retrieved 6 September 2018.
  6. Mistr hlásí posilu. Do Plzně míří Kayamba, podzim dokončí v Opavě". iDNES.cz. 6 September 2018. Retrieved 6 September 2018.
  7. Angola v DR Congo game report". ESPN. 17 November 2020.
  8. Hráč měsíce Kayamba: Přezdívku Mireček jsem přijal, díky fanouškům jsem nahoře. Nabídky z ligyodmítl". FORTUNA:NÁRODNÍ LIGA. Retrieved 2 September 2018.

Hanyoyin hadi na waje

gyara sashe