Jamilur Reza Choudhury
Dokta Jamilur Reza Choudhury (15 ga watan Nuwamba shekara ta 1942 zuwa 28 ga watan Afrilu shekara ta alif dubu biyu da a shirin 2020) ya kasance injiniyan farar hula na kasar Bangladesh, farfesa ne, kuma mai bincike, kuma mai ba da shawara kan ilimi. Ya kasance mai ba da shawara (Minista) a Gwamnatin Kula ta kasar Bangladesh a watan (Afrilu zuwa watan Yuni shekara ta 1996). [1] Ya kasance mataimakin shugaban Jami'ar BRAC kuma tsohon mataimakin Jami'ar Asiya Pacific. [2][3] Ya kuma kasance shugaban kwamitin wasannin Olympics a kasar Bangladesh daga shekara ta alif dubu dubu biyu da ukku 2003. Gwamnatin kasar Bangladesh ta ba shi kyautar Ekushey Padak a cikin rukunin kimiyya da fasaha a shekarar ta alif dubu biyu da sha bakwai 2017. Gwamnatin kaaar Bangladesh ta gabatar da shi a matsayin Farfesa na kasa a shekarar a shekara ta alif dubu biyu da sha takwas 2018.
Jamilur Reza Choudhury | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Sylhet (en) , 15 Nuwamba, 1943 |
ƙasa |
Bangladash British Raj (en) Pakistan |
Harshen uwa | Bangla |
Mutuwa | 28 ga Afirilu, 2020 |
Ƴan uwa | |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta |
University of Southampton (en) Mymensingh Zilla School (en) Bangladesh University of Engineering and Technology (en) Dhaka College (en) St Gregory's School (en) |
Harsuna |
Bangla Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | injiniya da civil engineer (en) |
Wurin aiki | Dhaka |
Kyaututtuka |
Rayuwar shi ta farko da asali
gyara sasheAn haifi Choudhury a Sylhet (a lokacin mulkin mallaka a kasar Burtaniya) a ranar 15 ga watan Nuwamba shekara ta 1943. Mahaifinsa, Abid Reza Choudhury (1905-1991), injiniyan farar hula ne wanda ya yi hijira zuwa Dhaka a shekara ta 1952 (bayan Rarraba Indiya) daga Rangauty, wani yanki na karkara na Hailakandi (Assam, Indiya). Abid shine Musulmi na farko da ya kammala karatu daga Jami'ar Injiniya da Kimiyya ta Bengal, a shekara ta 1929. Mahaifiyarsa, Hayatun Nessa Choudhury (née Laskor) (shekara ta 1922 zuw shekara ta 2010) ta kasance mai kula da gida, daga yankin Nitainagar na Hailakandi . Jamilur ita ce ta tsakiya a cikin 'yan uwa biyar. [ana buƙatar hujja][<span title="This claim needs references to reliable sources. (April 2020)">citation needed</span>]
Choudhury ya fara makaranta a shekara ta 1950 (lokacin ya dan shekara 6 )a Makarantar Mymensingh Zilla . Bayan da yan uwa sa suka koma Dhaka daga Mymensingh a shekara ta 1952, ya koma makarantar sakandaren gwamnati ta Nawabpur, kuma ya sake komawa makarantar Katolika mai zaman kanta, St Gregory's High School, a shekara ta 1953. Ya wuce jarrabawar shiga daga makarantar sakandaren Sylhet Government Pilot. Ya halarci Kwalejin Dhaka daga shekara ta 1957 zuwa 1959 kuma ya sami shidar digiri sa na farko a ban garan Kimiyya (Civil Engineering ) daga Jami'ar Injiniya da Fasaha ta kasar Bangladesh (BUET) a shekarar 1963. Bayan kammala karatunsa daga BUET (First Class First with Honours), ya zama malami a Sashen Injiniyanci a wannan shekarar. Ya sami digiri na biyu na Kimiyya a cikin Injiniya (ƙwarewar injiniya) a shekara ta 1965 da Ph.D. a cikin injiniyan tsari a shekara ta 1968, duka a Jami'ar Southampton.
An ba Choudhury digiri na girmamawa na Doctor of Engineering (Honoris Causa) daga Jami'ar Manchester a ranar 20 ga watan Oktoba a shekara ta alif dubu biyu da a shirin 2010 - mutum na farko kuma dan asalin kasar Bangladesh da ya karbi wannan girmamawa daga Jami'an kasar Burtaniya. <ref name="uap">"Profile of Prof. Dr. Jamilur Reza Choudhury". University of Asia Pacific. Archived from the original on 30 March 2013. Retrieved 18 December 2013."Profile of Prof. Dr. Jamilur Reza Choudhury". University of Asia Pacific. Archived from the original on 30 March 2013. Retrieved 18 December 2013.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Create professionals in disaster management". The Daily Star (in Turanci). 2008-08-15. Retrieved 2020-04-30.
- ↑ "Professor Jamilur Reza Choudhury, PhD was the first Vice Chancellor of BRAC University". BRAC University Website. 19 April 2015.
- ↑ "Profile of Prof. Dr. Jamilur Reza Choudhury". University of Asia Pacific. Archived from the original on 30 March 2013. Retrieved 18 December 2013.