Jami'ar Tarayya, Wukari

Jami'ar gwamnatin tarayya da ke Wukari Jihar Taraba, Nijeriya

An kafa Jami'ar Tarayya da ke Wukari a shekarar 2011 a ƙarƙashin gwamnatin tarayyar Najeriya bisa ga jagorancin shugaba Goodluck Jonathan, makarantar ta kasance ɗaya daga cikin makarantu tara da aka kafa a lokacin.[1] Jami'ar tarayya da ke Wukari na cikin garin da ake kira Wukari a Jihar Taraba a tarayyar Najeriya.[2]

Jami'ar Tarayya, Wukari
Bayanai
Suna a hukumance
Federal University Wukari
Iri jami'a da public university (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Harshen amfani Turanci
Mulki
Hedkwata Wukari
Tarihi
Ƙirƙira 2011
fuwukari.edu.ng

Makarantu gyara sashe

Jami’ar Tarayya, Wukari tana da kwalejoji uku da suka kunshi sassa 25:[3]

  • Faculty of Agriculture da Life Sciences
  • Faculty of Humanities, Management, da Social Sciences
  • Faculty of Pure and Applied Sciences

Mataimakan Shugaban Jami'ar gyara sashe

Jami’ar tarayya da ke Wukari tun kafuwarta tana da mataimakan shugabanin jami’ar da suka kasance shugabannin gudanarwa na cibiyar. A watan Maris na shekarar 2016 ne aka naɗa Farfesa Abubakar Kundiri a matsayin mataimakin shugaban cibiyar na 2, a lokacin da yake riƙe da muƙamin mataimakin shugaban jami’ar, yawancin kwasa-kwasan da ake yi a makarantar sun samu karɓuwa.[4][5] Farfesa Abubakar Musa Kundiri ya kasance mataimakin shugaban jami'ar na tsawon shekaru biyar (2016 - 2021), har zuwa watan Janairu, 2021 lokacin da Farfesa Jude Rabo, farfesa a fannin dabbobi, bayan an tantance shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma aka naɗa shi a matsayin sabon mataimakin. Shugaban cibiyar ya gaji Farfesa Abubakar Musa Kundiri.[6][7]

Matsayi gyara sashe

Jami'ar Tarayya, Wukari ta kasance a matsayi na 87 mafi kyawun jami'a a Najeriya a watan Janairun 2020, daga Webometrics.[8]

Duba kuma gyara sashe

  • Jerin Jami'o'in Najeriya

Manazarta gyara sashe

  1. "SPECIAL REPORT: Eight years after, new federal university in Taraba faces infrastructural shortage | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2019-10-18. Retrieved 2022-01-18.
  2. "Federal University, Wukari | Ranking & Review". www.4icu.org. Retrieved 2022-01-18.
  3. "We are making Federal University Wukari a world-class education center — Vice Chancellor". Vanguard News (in Turanci). 2020-01-30. Retrieved 2022-01-18.
  4. "My legacies at Federal University of Wukari can't be forgotten – Prof. Kundiri". Punch Newspapers (in Turanci). 2019-03-31. Retrieved 2022-01-18.
  5. "We are making Federal University Wukari a world-class education center — Vice Chancellor". Vanguard News (in Turanci). 2020-01-30. Retrieved 2022-01-18.
  6. "Prof Rabo Emerges New Vice-Chancellor Fed University, Wukari". Daily Trust (in Turanci). 2021-01-21. Retrieved 2022-01-18.
  7. "Federal University, Wukari gets new vice chancellor" (in Turanci). 2021-01-21. Retrieved 2022-01-18.
  8. "Search | Ranking Web of Universities: Webometrics ranks 30000 institutions". www.webometrics.info. Retrieved 2022-01-18.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe