Pen Resource Academy (PRA) ce ta kafa jami’ar Pen Resource,[1] wacce ke Jihar Gombe a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya. Jami'ar na ɗaya daga cikin sabbin jami'o'i masu zaman kansu goma sha biyu da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da su a cikin Afrilu 6, 2022,[2][3][4]kuma Hukumar Jami'o'in Najeriya (NUC) ta ba shi lasisi a watan Mayu 2022.[2]

Jami'ar Pen Resource
Bayanai
Iri jami'a
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 6 ga Afirilu, 2022
pru.edu.ng

Tarihi gyara sashe

Jami'ar Pen Resource ita ce jami'a mai zaman kanta ta farko a jihar Gombe kuma ta uku a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya [5] . Dr Sani Jauro [6] ne ya kafa makarantar a karkashin makarantar Pen Resource Academy[1]. Makarantar tana a Lafiyawo a kan titin Gombe zuwa Bauchi, Gombe, jihar Gombe kuma tana mai da hankali kan bunkasa karni na ashirin da daya da fasahar dijital na daliban.[7]

Sashe gyara sashe

Jami'ar tana da sashe uku wadanda su ne;

  • Makarantar Kimiyya da Kwamfuta
  • Kwalejin Sadarwa, Gudanarwa da kimiyyar zamantakewa[1]

Mataimakin Shugaban Jami'ar gyara sashe

Farfesa Ogbaji Igoli, Farfesan Kimiyyar sinadarai da ke zaune a Burtaniya, shi ne mataimakin shugaban jami’ar ta farko.[8]

Shugaban Jami'ar gyara sashe

Dr Sani Jauro shine Shugaba kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami'ar Pen Resource.[8]

Nassoshi gyara sashe