James Moorhouse (ɗan siyasa)
Cecil James Olaf Moorhouse (1 Janairu 1924 - 6 Janairu 2014) ɗan siyasan Burtaniya ne kuma tsohon ɗan Majalisa a Tarayyar Turai. [1]
Karatu
gyara sasheYayi karatu a St Paul's School, London, King's College London (BSc Eng, 1945) da Imperial College Londo, inda a nan yayi difloma a fannin advanced aeronautics.[2]
Siyasa
gyara sasheYayi aiki a matsayin ɗan majalisa a karkashin jam'iyyar Conservative na London ta Kudu daga 1979 zuwa 1984, kuma a matsayin MEP mai ra'ayin mazan jiya na London ta Kudu da Surrey East daga 1984 har zuwa Oktoba 1998 lokacin da "ya koma jam'iyyar Liberal Democrats bayan rashin yarda da manufofin Mr Hague kan kudin Euro ."[3]
Ya kasance a Majalisar Tarayyar Turai a matsayin MEP na Liberal Democrat na London ta Kudu da Surrey East har zuwa 1999.
Mutuwa
gyara sasheYa mutu ranar 6 ga watan Janairu, 2014
Manazarta
gyara sashe- ↑ James MOORHOUSE Obituary
- ↑ Dod's Parliamentary Companion. 1999.
- ↑ "MEPs quit 'euro-sceptic' Tory party". BBC News. 19 January 1999. Retrieved 15 November 2009.