PRP ɗaya ce daga cikin Jam'iyyun siyasar Najeriya wacce ta kwana biyu. Anyi ƙoƙarin fara kafa wannan jama’iyya a cikin jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu wato (second republic) da turanci, a cikin jihar Kano. Jama’iyyar ta samu nasarar cin zaɓen manyan jahohin arewacin Najeriya guda biyu daga cikin goma na wancan shekarun. Jahohin sune; Kaduna da kano kafin a cire jihar Katsina cikin Kaduna, haka kaso kafin a cire jihar Jigawa su ne jahohin da jama’iyyar ta PRP ta samu daman nasarar cin zaɓe a wancan lokacin (1971).

Tsarin tutar ta gyara sashe

Anyi ma tutar jam'iyyar PRP ƙawa da makulli a tsakiyar ta sannan samanta launin ja haka ƙasanta launin baƙi

Tarihi gyara sashe

Wanda ya Kafata gyara sashe

Marigayi malam Aminu Kano, wanda aka fi sani da limamin canji ko jagoran talakawa, shi ne ya jagoranci kafa jama’iyyar bayan samun saɓani da ya yi da ƙungiyar masu kishin ƙasa (National Movement).

Kafata gyara sashe

An kafa wannan jama’iyya ta PRP a cikin shekarar (1978) biyowa bayan janye takunkunmin siyasa da gwamnatin sojon tarayyar Najeriya ta yi a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1978, wacce shugaba olusegun Obasanjo ke jagoranta a lokacin bayan rasuwar Janar Murtala Mohammed. Takunkumin da ya ɗauki tsawon shekaru goma sha biyu (15/01/1966 – 1/10/1978).

Rikice-rikice gyara sashe

Ɓaraka da aka samu a cikin haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu kishin ƙasa National Movement, tsakanin wasu daga cikin shugabanninta da kuma malam Aminu Kano a ɗaya ɓangaren, a yunƙurin mayar da ƙungiyar jama’iyyar siyasa shi ne abin da ya kai ga dasa ɗan-ba na kafa jama’iyyar ta PRP. Saboda haka ita wannan jama’iyya ta PRP da ƙafafunta biyu aka haifeta; ba a yi goyon cikinta ba bare a yi renonta har ta yi rarrafe. Ko da ma an yin ta wata fuska, to ba kamar yadda aka saba ba. Saboda haka nema ta samu damar yin tserereniya da yayyenta. Har ma ta iya tserewa wasu daga cikinsu. Bayan an kafa wannan ƙungiya a zauren majalisar sake nazarin sabon tsarin mulkin Najeriya, sai ya zama mambobinta a matakin farko ‘yan waccar majalisa ne zalla. Amma daga baya sai aka gabatar da ita ga ƙungiyar dattawan arewa Northern Consultative Forum. Marigayi malam Aminu Kano, mamba ne a waccar majalisa ta sake nazarin sabon tsarin mulki, sannan kuma shugaban kwamatin rubuta tsarin mulkin. Ƙari a kan haka kuma, shi mamba ne na wannan ƙungiya ta dattawan arewa. Saboda haka, sai ya bayar da shawara ga dukkan ‘yan siyasar arewa jam'iyyar NEPU, jam'iyyar NPC, jam'iyyar MBC da sauransu da cewa su shiga wannan ƙungiya baki ɗayansu. Ya ƙara da bayanin cewa, waɗanda suka kafa waccar ƙungiya ta kishin ƙasa, ba cikakkun ‘yan siyasa ba ne a wancan lokacin. Saboda haka, idan har ƙungiyar ta zama jama’iyya, to su za su fara cin moriyar abun. Saboda su za su zama shugabannin jama’aiyyar. Ganau ba jiyau ba, Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya ce, “wannan harsashe na malam Aminu Kano, shi ne kuma abin da ya tabbata daga baya”. Shi kuwa Alhaji Salihu Tanko Yakasai, makusancin malam Aminu Kano ne. Kusanci kuma na haƙiƙa. Saboda a wannan lokaci dukkan wasu tarurruka da shi Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya ke halarta, yana zuwa ne a matsayin wakilin malam Aminu Kano da kuma tsohuwar jama’iyyarsu ta NEPU.

Rugujewar jam'iyyar PRP gyara sashe

Rugujewar jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu; wato rushewar jamhuriyya ta biyu a siyasar Najeriya, shi ne abin da ya kawo ƙarshen wannan jama’iyya. Sai dai, tsohon gwamnanta na Kaduna, Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa, ya sake sabunta ta a wannan jamhuriyyar da yanzu ake cikinta a siyasar Najeriya. Tsawon ran wannan jama’iyya ta PRP shi ne tsawon ran jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu. Wanda kuma hakan ta faru ne bayan sanarwar rushe jamhuriyyar ta biyu da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1983. Wannan shi ne bayani game da farko da kuma ƙarshen jama’iyyar PRP a jamhuriyya ta biyu.

Manazarta gyara sashe