Iruka Okeke Ta kasance masaniya ce ƴar Najeriya wadda ta yi nazari kan kwayoyin halittar cuta masu haddasa cututtuka irin su E. coli. Ta kuma yi bincike kan hanyoyin inganta ayyukan ɗakin gwaje-gwaje na microbiology a Afirka. Ta kasance abokiyar Kwalejin Kimiyya ta Najeriya da Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Afirka.

Iruka Okeke
Rayuwa
Haihuwa Ingila, 1970 (53/54 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
University of Maryland (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a microbiologist (en) Fassara, biologist (en) Fassara da university teacher (en) Fassara
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Okeke a Ingila ga iyayen ƙasar Najeriya. Daga baya ta koma Najeriya don shiga makarantar sakandare.[1] Ta halarci Jami'ar Obafemi Awolowo, Najeriya, inda ta sami digirin farko har zuwa na ukku-( BPharm, MSc, da PhD).[2] A matsayinta na PhD ta yi shekara guda a Cibiyar Ci gaban Alurar riga kafi, Jami'ar Maryland a matsayin Masaniyar shirin Fulbright Program.[3]

Aikin bincike

gyara sashe

Okeke ta gudanar da bincikenta na digiri na biyu a Jami'ar Maryland, Amurka da Jami'ar Uppsala, Sweden. A cikin shekarar 2000 ta koma Jami'ar Bradford, Ingila, a matsayin memba ta (teaching faculty).[ana buƙatar hujja] Daga nan ta koma Kwalejin Haverford, Amurka a shekaran 2002 a matsayin Matemakiyar Farfesa kafin ta zama cikakkiyar Farfesa a 2014.[3] A lokacin da ta ke Haverford ta kasance (Branco Weiss Fellow) na kungiyar (Society of Science) tsakanin 2004-2009, kuma (Fellow of the Institute for Advanced Studies, Berlin) daga 2010-11.[3]

Binciken ta ya mayar da hankali kan yin amfani da kwayoyin halitta don fahimtar ilimin kwayoyin cuta, ikon cutukan, pathogenesis da juriya na kwayoyin cuta na ciki.[4] Ta yi nazari kan sunadaran E. coli kuma ta bayyana yadda waɗannan sunadaran ke taimakawa ƙwayoyin cuta su mallaki hanji.[1]

A cikin 2014, Okeke ya koma Jami'ar Ibadan, Najeriya, tana samun goyon bayan Hukumar Binciken Likitoci ta Burtaniya da Sashen Raya Kasashe na Burtaniya a matsayin Jagoran Bincike na Afirka.[3] A cikin 2019 an ba ta kuɗi don binciken magunguna na Afirka da gano yuwuwar magungunan ƙwayoyin cuta daga gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation.[5][6]

Kyaututtuka da Karramawa

gyara sashe
  • Elected as a fellow of The African Academy of Science in 2018.[3]
  • Elected as a fellow of the Nigerian Academy of Science in 2018.[7]

Rayuwa ta kashin kai

gyara sashe

Okeke tayi Aure kuma tana da ƴa mace.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 Foley, Denise (2014). "Faculty Profile". Haverford. Retrieved 2019-12-03.
  2. "Dr. Iruka N. Okeke new Editor-in-Chief". ASLM (in Turanci). Retrieved 2019-12-03.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 "Okeke Iruka". www.aasciences.africa. The African Academy of Sciences. Archived from the original on 2023-03-31. Retrieved 2019-12-03.
  4. "Iruka Okeke | STS Infrastructures". stsinfrastructures.org. Retrieved 2019-12-03.
  5. "African innovators discovering new drugs for diseases endemic to Africa". www.aasciences.africa. The African Academy of Sciences. Archived from the original on 2019-12-03. Retrieved 2019-12-03.
  6. "Minimal Genomics Lab for AMR Surveillance and Diagnostics in Provincial Low-income Settings | Grand Challenges". gcgh.grandchallenges.org. Retrieved 2019-12-03.
  7. "Fellows of the Academy | The Nigerian Academy of Science" (in Turanci). Retrieved 2019-12-03.