Idris Shaaba Jimada kwararren malami ne dan Najeriya kuma Daraktan Arewa House Kaduna, malami ne a bangaran tarihi kuma mataimakin shugaban sashen koyar da fasaha a Jami’ar Ahmadu Bello . An nada Jimada a matsayin Daraktan Arewa House bayan zamanin Farfesa Sule Bello ya kare. Arewa House tsohuwar gida ce ta yankin arewacin Najeriya kuma gidan Premier Sir Ahmadu Bello, yanzu ita ce cibiyar bincike da adana tarihin Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya gidan tana kula da tattatara tarihi nahi Arewacin Najeriya. [1][2][3]

Idris Shaaba Jimada
Rayuwa
Haihuwa Kwara, 1984 (39/40 shekaru)
Sana'a

Farkon rayuwa da Ilimi

gyara sashe

Jimada ya samo asali ne daga Jihar Kwara, malami ne a fannin Tarihi daga Jami'ar Ilorin. Yana da MA da PhD daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya . Har ila yau, yana da sha'awa game da dangantakar abokantaka, da na zamani, na nazarin ƙasa da na ƙasa game da ƙungiyoyi na siyasa da zamantakewa.[4][5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Prof Jimada is now Director of Arewa House". Daily Trust (in Turanci). 2018-02-23. Retrieved 2020-04-08.
  2. "Arewa House to honour notable men of integrity". Daily Trust (in Turanci). 2018-09-03. Retrieved 2020-04-08.
  3. "Buhari canvasses sound education sector built on values". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2019-07-10. Retrieved 2020-04-08.
  4. "Buhari Reviving Education". aitonline.tv (in Turanci). Retrieved 2020-04-09.
  5. Malumfashi, Muhammad (2019-07-11). "Yadda cibiyar tarihin Arewa ke shirin karrama Shugaban kasa Buhari har abada". Legit.ng - Nigeria news. Archived from the original on 2020-08-03. Retrieved 2020-04-09.