Ibrahim Narambada ko Narambada kamar yadda a kafi sanin sa (1890-1963).

Ibrahim Narambada
Rayuwa
Haihuwa 1890
ƙasa Nijar
Mutuwa 1963
Sana'a
Sana'a mawaƙi

An haifi Narambada a shekarar 1890, Mahaifinsa, Maidangwale dan asalin Jamhuriyar Nijar ne, a kasar Filinge, amma ya zo garin Tubali ya kuma zauna kuma a nan ya auri mahaifiyar Narambada. Maidangwale dai shahararren dan dambe ne. An haifi Narambada a garin Tubali kuma a nan ya yi Karatun, ya yi rayuwarsa duka. Mahaifiyar Narambada kuwa makidiya ce, don haka, za'a iya cewa ya yi gadon kida ne daga wurinta.

Suna Narambada

gyara sashe

Ya samu sunan Narambada ne dalilin wata karyarsa da ake ce wa Rambada, don haka, sai aka yi masa lakabi da Narambada.

Fara tashe

gyara sashe

Tarihi ya nuna cewa Narambada ya budi ido ne ya ga kayan kidan kotso a dakin mahaifiyarsa, wanda ita ma na mahaifinta ne ta yi gado. Narambada ya fara ne da kidan Noma Wata rana sai ya yi kidan noman kauyensu a fadar Sarkin Gobir na garin Isa (jahar Sokoto a yanzu) Da aka ji dadin wakar da kuma yadda yake da kwarewa da hikima, sai aka mayar da shi birni ya zamo makadin Gobir. Don haka, ya cigaba da yi wa Amadu Sarkin Gobir waka.

Narambada ya yi wakoki da dama a rayuwarsa kamar su "Ya ci maza ya kwan yana shiri, uban zakara, dodo na Ummaru" da "Batun da akai na yau babu Sarki yau irin ka,/ Jikan Bello arna suna shakkak ka" da "Alkalin Alkalai ta aiki nai da tsari" da "Masu gari mazan gabas tsayayye, Sarkin Rwahi ya wuce a ram mai" da dai sauransu. Farfesa Aliyu Bunza na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ya ce "a ganina dukkanin kasar Zamfara ba a yi mawakin da ya kai Narambada ba. Kuma ba a kasarsa kawai yake waka ba. Ma'anar, duk duniyar Kasar Hausa." Yawancin wakokinsa ya yi amfani da kalamai na hikima da zalaka, wanda ya sa wakokinsa suka fita daban da na sauran mawakan Hausa. Misali a wakar da ya yi wa Sarkin Gobir, ya yi amfani da salo na hikima da fasaha inda yake cewa: "Na aje karya ko ina kidi, Na bar karya ko ina kidi, Nai sitting, saba'in ni ka hwata, Mai saba'in yai karya ana ta zunde nai, Ko yaran da ag garai du wawwatse mashi sukai, Yana yawo shi dai baram-baram".

Adadin Wakokin sa

gyara sashe

Babu wani cikakken adadi na wakokin da Narambada ya yi, amma Farfesa Bunza ya ce "Wasu su kan ce ya yi wakoki sun kai dari ko dari da wani abu amma iyakar binciken da mu ka yi, kusan sama da shekaru ashirin da wani abu gaskiya ni hamsin na samu, wadanda na rubuta da kai na, na saurara, na tabbatar sun rubutu, na ajiye." Farfesa Bunza ya ce ko wane irin mawaki da irin fasaha da hikima da zalaka da Allah ya hore masa. "Allah ya hore masa waka, amma shi Narambada ba a nan take yake yin ta ba. Idan zai yi maka waka, zai je gida ya tsara ta, a yinin da zai yi wakar, ba zai yi hulda da kowa ba. "Haka wasu yaransa suka shaida mana. In ya kare tsara ta, sai ya kira yaransa, sai su rera. Wakar Narambada in zai yi ta, zuba waka ake zube-ban-kwarya," in ji Farfesa Bunza. Wato dai Narambada ba ya rubuta waka sai dai ya tsara ta a zuciyarsa. Idan ya gama tsarawa sai ya gaya wa yaransa ya ce shaida masu amshin wakar su yi ta maimaitawa har ya zauna masu, sannan a je a rera ta. Akwai wakar Narambada da ya yi ikirarin cewa ba zai mutu ba. Ya ce: "Narambada ba ya zuwa lahira, ko ya je dawowa ya kai, Hwadawa ku bugan in buge ku, Mui ta fadan mu gidan duniya, kun san ba a hwada lahira, kun san kuka zuwa lahira, Narambada ba ya zuwa lahira, ko ya je dawowa ya kai, gama kun san dauke mai a kai." Masana sun fassara wadannan kalamai na Narambada a matsayin cewa dalilin wakokinsa ba zai "mutu" ba tunda har yanzu tsawon shekaru bayan rasuwarsa ana sauraren wakokinsa. Farfesa Bunza ya ce "maganarsa ta tabbata. Fadawa ke mutuwa- da Bafade ya mutu, a fada an manta da shi. Da Sarki ya mutu, a fada an manta da shi, an yi wani. Amma idan zakaran mawaka ya mutu, ba mutuwa ya yi ba. "Har yanzu ga Narambada ba shi duniya, ana maganarsa, ana jin maganarsa. Ina fadawa suke? Saboda haka duk wani mawaki da ya san kan sa, ya yi luguden wakar, to bai mutu ba, yana nan a raye!" Ana iya cewa wannan na daga cikin irin hikima da basira da iya salon magana da Allah Ya bai wa Alhaji Ibrahim Narambada.


Manazarta

gyara sashe